Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Lahadi.
A bayanan da NCDC ta fitar, Legas ta samu karin mutun 70, Abuja 7, 3 a Katsina, Akwa Ibom 3, Jigawa 1, 1 a Bauchi, 1 a Barno.
Yanzu mutum 627 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 170 sun warke, 21 sun mutu.
Lagos- 376
FCT- 88
Kano- 37
Osun- 20
Oyo- 16
Edo- 15
Ogun- 12
Kwara- 9
Katsina- 12
Bauchi- 7
Kaduna- 6
Akwa Ibom- 9
Delta- 4
Ekiti- 4
Ondo- 3
Enugu- 2
Rivers-2
Niger- 2
Benue- 1
Anambra- 1
Jigawa – 1
Barno – 1
Wannan shine karo na farko da aka samu yawan mutane har sama da 80 da suka kamu a Najeriya. Jihohin Barno, Bauchi da Katsina duk sun samu rabon su a sakamakon gwajin da aka fitar ranar Lahadi.
Idan baa manta a ranar Asabar ne aka yi jana’izar suhagaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Marigayi Abba Kyari.
Abba Kyari na daga cikin wadanda suka rasu a dalilin kamuwa da cutar.
Ya rasu ranar Juma’a a Legas bayan fama da yayi da cutar na tsawon makonni biyu.
Wannan shine karon farko da za a bayyana wani ya kamu da cutar a jihar Barno.