Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Asabar.
A bayanan da NCDC ta fitar, Jihar Kano ta samu karin mutum 10, Legas 23, Abuja 12, 5 a Kwara, Oyo 1, 2 a Ogun da 1 a Ekiti.
Yanzu mutum 542 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 166 sun warke, 19 sun mutu.
Lagos- 306
FCT- 81
Kano- 37
Osun- 20
Oyo- 16
Edo- 15
Ogun- 12
Kwara- 9
Katsina- 9
Bauchi- 6
Kaduna- 6
Akwa Ibom- 6
Delta- 4
Ekiti- 4
Ondo- 3
Enugu- 2
Rivers-2
Niger- 2
Benue- 1
Anambra- 1
Idan ba a manta ba shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) Chikwe Ihekweazu ya koka kan yadda mutane ke kyamatar wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.
Ya ce nuna wariya da ake yi wa wadannan ke dauke da cutar na dawo wa hukumar da hannun agogo baya a aiyukkan da suke yi na hana yaduwar a Najeriya.
Ihekweazu ya ce NCDC na kokarin ganin ta kara yawan mutanen da ake yi wa gwajin cutar a kasar nan amma hakan ba zai yiwu ba idan ana ana kyamatar su a duk inda suke.
Ya ce mutane za su fara guje wa yin gwajin cutar da boye wa ma’aikatan kiwon lafiya saboda haka.