COVID-19: Yobe za ta tallafawa talakawa da gajiyayyu 18,000

0

Gwamnatin jihar Yobe ta bayyaa cewa za ta tallafawa gajiyayyu da talakawa 18,000 a jihar.

Gwamnati ta ce yin haka zai taimaka wajen rage radadin talauci ga mutane musamman a watan Ramadan da wannan lokaci na annobar cutar coronavirus.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar (YOSEMA) Mohammed Goje, ya Sanar da haka a hira da yayi da manema labarai a garin Damaturu.

Ya ce gwamnati za ta hada da ‘yan gudun hijira dake jihar domin tallafa musu.

YOSEMA za ta yi amfani da malaman addini, kananan hukumomi, manema labarai da jami’an tsoro domin ganin tallafin ya isa hannun mutanen da ya kamata.

Goje ya ce Kungiya mai zaman kanta ‘Victims Support Funds (VSF) ta ba da gudunmawar abinci da magunguna domin tallafawa mutane a jihar.

A yanzu dai mutum 407 ne ke dauke da coronavirus a Najeriya.

Daga ciki an sallami 122, 12 sun mutu.

Idan ba a manta ba ranar 15 ga watan Afrilu ne ma’aikatar Harkokin Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma, ta ce kashi 25 bisa 100 ne kadai na ‘yan Najeriya za su amfana da tallafin kudade da abincin rage radadin kunci da za a raba kwanan nan.

Ma’aikatar ta ce wannan karon za a damka rabon abincin ne ga gwamnatocin jihohi, domin gudun kada a sake samun cikas din da aka samu a rabon da aka yi na baya.

A yanzu dai mutane 407 ne ke dauke da coronavirus a Najeriya. Daga ciki an sallami 122 sun warke sannan 12 sun mutu.

Share.

game da Author