Tun bayan bullowar wannan cuta ta COVID-19, a kasar mu Najeriya, Gwamnati da hukumomi da ke da alhakin bada kulawa don tsagaitar da yaduwar cutarke ta taka muhimmiyar rawa don ganin an shawo kan lamarin.
Gwamnatocin jihohi da dama sun dauki matakan rife iyakokin jihohin su domin takaita zirga zirga don bin shawarwarin da dokokin da hukumar kiyaye lafiya ta gindaya ta bada don dakile yaduwar wannan cuta.
Haka zalika attajiran yan kasuwa, da bankuna, kungiyoyi masu zaman kansu da kuma wasu yan kishin kasa, suma sun yi kokari wajen bada gudumuwar tallafin kudi, raba kayan abinci ga mabukata da sauran su.
Duk da fama da rashin samun wuraren killache mutane a fadin kasar da kayan gwajin mutane da ake zargin suna dauke da wanan cuta ta COVID -19, da kuma isar sun kayan aiki da za akula da wanda suka kamu da wannan cutar.
An samu jajurtattun mutane ‘yan kishin kasa da suka yi kokari wajen kera naurar taya numfashi (ventilator), da kuma hada man tsaftace hannu (hand sanitizer), da takunkumin fuska (face mask), daga bangarori da dama a fadin kasar nan, wanda abun a yaba ne.
Toh amma fa gwamnati haryan zu bata bada gudunmawa ma wadannan jajirtattun mutane ba don su ci gaba da kera wa inan naurorin domin a ci gaba da rabawa ga wuraren killace masu dauke da ciwon dake fadin kasar wanda hakan bai dace ba in har an tabbatar dacewa naurorin da suka kera yana da inganci kuma za a iya amfani dasu.
Ba ina nufin gwamnati ta dakatar ko kuma kada ta siyo wadannan naurorin bane daga kasashen ketare , abin nufi shine tallafawa wa inan jajurtatun mutane zai tai maka sosai gun habaka kera naurorin da kuma samar da masana’anta a nan kasar, kuma zai bada damar samun aiki ga matasa wanda har zai iya kai ga watarana muma mu talafawa kasashen da ke da bukata.
In muka dau misali dacewa in wadannan mutane zasu rika kera akalla na’urori guda 10 a kullum toh a wata daya kacal zasu kera na’urori guda 300, kila ma yafi hakan yawa, kun ga ai ba karamin ci gaba aka samu ba.
Rashin tallafawa irin jajirtatun mutanen nan kesa wasu masu fasahar kere kere ke fasa kera abubuwa da dama wanda kasa zata amfana sannan tayi alfahari dasu.
A karshe ina kira ga gwamnati da kuma masu kula da wannan fannin suyi hobbasa wajen daukan matakan da ya dace dan habbaka fannin kere-kere a kasar mu Najeriya.
Sani Adamu, Dalibi mai karantu a fannin sarafa da ajiyar kudi a jamiar jihar Kaduna.
Discussion about this post