Adadin yawan mutanen dake dauke da cutar coronavirus a duniya ya karu daga miliyan daya zuwa sama da miliyan biyu a cikin makonnin biyu.
Mutanen da cutar ta kashe a duniya ya karu zuwa 126,000.
Binciken ya nuna cewa a cikin kwanaki 13 mutane 76,000 suka mutu a duniya.
Har yanzu babu maganin coronavirus amma wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya na hasashen cewa an samu ragowa a yadda cutar ke yaduwa.
Haka ya sa wasu kasashen duniya da suka samu saukin yaduwar cutar suka fara dauka matakan farfado da halin rayuwa da tattalin arziki kasashen su yadda suke a da.
Sai dai kuma Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta nuna matukar damuwa dangane da yadda wasu kasashe ke ta hankoron janye dokar zaman gida domin hana fantsamar cutar Coronavirus.
WHO ta ce gaggauta janye dokar zai iya sa cutar ta sake danno kai a cikin kasashen da suka janye dokar ta zaman gida.
Kasashen Faransa,Spaniya,Italiya, UK, Amurka da Kudu maso Gabashin Asia na cikin kasashen duniya da coronavirus ta yi wa kamu mai tsanani.
Bisa ga sakamakon binciken da Worldometer ta gabatar ranar Laraba ya nuna cewa mutane 2,000,728 ne ke dauke da cutar a duniya.
AMURKA
A cikin awa 24 mutum 2,400 suka mutu a kasar Amurka.
Worldometer ta ce a kasar mutum 614, 246 suka kamu da cutar.
A New York mutum 200,000 ne ke dauke da cutar.
A yanzu dai mutane 126,776 suka mutu a sanadiyyar kamuwa da coronavirus a duniya.
Wasu kwararrun likitoci sun ce akwai yiwuwar cutar zai kashe mutane da dama a duniya ba tare da an yi mutu gwajin cutar ba saboda rashin isassun kayan gwajin cutar.
NAHIYAR AFRIKA
Sama da mutane 16,000 na dauke da coronavirus a Nahiyar Afrika inda haka yasa kasashen daukan tsauraran matakan hana yaduwar cutar.
Cutar na gab da mamaye kasashen dake Nahiyar Afrika domin kuwa kasashe biyu ne kawai suka rage da ba su kamu da cutar ba.
Kasar Algeria ce kasar dake kan gaba wajen samun yawan mutanen da suka mutu a dalilin kamuwa da cutar.
Algeria
326 -sun mutu
2000 – sun kamu.
Masar
178 – sun mutu.
2,350 – sun kamu.
Morocco.
126 – sun mutu.
1,888 – na dauke da cutar.
Afrika ta Kudu.
27 -sun mutu.
2,400 – na dauke da cutar.
Najeriya
362 – Suka kamu
11 – Sun mutu
A ranar Litini ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kara kara wa’adin kwanakin zaman gida dole a Abuja, Legas da Ogun da Kwanaki 14.
Bihar ya ce ya yi haka ne domin a samu nasaran dakile yaduwar cutar a kasan.
Sai dai WHO ta ce tana gargantuan yaduwar cutar a Nahiyar Afirka musamman yadda fannin kiwon lafiyar kasashen Afrika ke gab da rugujewa.