COVID-19: Mutum daya ya mutu a jihar Kano, wasu da yawa sun kamu

0

Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Kano ta Sanar cewa mutum daya ya rasu a dalilin kamuwa da cutar coronavirus a jihar ranar Alhamis.

Ma’aikatar ta kuma sanar cewa ta samu karin mutum 12 da suka kamu da cutar inda haka ya kawo jimmlar mutanen da suka kamu da cutar zuwa 21 a jihar duk a cikin mako daya.

Wannan sanarwa ta fito ne bayan hukumar NCDC ta Sanar cewa mutane 16 ne suka kamu da cutar a jihar Kano.

A ranar Alhamis kakakin ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Kano Hadiza Namadi ta ce bata da masaniya game da sabanin yawan adadin wadanda suka kamu da cutar a jihar Kano.

Ta ce kwamitin hana yaduwar cutar coronavirus na jihar ne ke da sakamakon gwajin cutar da aka yi a jihar.

Shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar na jihar Hassan Fagge ya ce yanzu ana iya gudanar da gwajin cutar a jihar sannan akwai yiwuwar an samu karin ne bayan sanarwan da hukumar NCDC ta yi.

Haka ya nuna cewa mutum 20 ke kwance a asibiti.

Idan ba a manta ba, ranar Talata ne gwamna jihar Kano Abdullahi Ganduje ya saka dokar zaman gida dole a jihar.

Ganduje ya ce dokar zai fara aiki ne ranar Alhamis daga karfe 10 na dare kuma na tsawon kwanaki 7.

Ya umarci Jami’an tsoro za su hukunta duk wanda aka kama ya karya wannan doka da gwamnati ta saka.

Kafin cutar ta bullo a jihar gwamnati ta toshe duk iyakokin shiga jihar a matsayin matakan hana shigowa da coronavirus jihar.

Share.

game da Author