Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) a Brazzaville kasar Kongo ta bayyana cewa adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar a Nahiyar Afrika ya wuce mutum 14,000.
WHO ta sanar da haka a shafinta na tiwita @WHOAFRO a wannan mako.
Kungiyar ta ce a yanzu haka mutane 2,523 sun warke sannan 754 sun mutu a Afrika.
Kasashen Afrika ta Kudu, Algeria da Kamaru na cikin kasashen da cutar ta yi wa mummunar kamu.
Afrika ta Kudu
2,173 – Ke dauke da cutar
25 – sun mutu.
Algeria
1,914 – Ke dauke da cutar.
293 – sun mutu
Cameroon
803 – sun kamu
10 – su mutu.
Who ta ce kasashen Sudan ta Kudu, Sao Tome da Principe, Burundi, Mauritania da Gabo Verde ne ke da karancin wadanda suka kamu.
Sudan ta Kudu mutane 4, mutum 4 Sao Tome sannan a Principe mutum 4.
Burundi mutum 5, Mauritania mutum 7 na dauke da cutar 1 ya mutu, Gabo Verde na da mutum 7, 1 ya mutu.
A Najeriya cutar ta bullo a jihohi 19 da Abuja sannan mutane 343 na dauke da cutar.
An sallami 91 sannan 10 sun mutu.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya hukumar WHO ta sanar cewa fiye da mutum 10, 000 na dauke da cutar fadin Afrika.
WHO ta ce a can baya cutar ta fi yin kamu a manyan biranen kasashen, amma yanzu ta kara fantsama cikin sauran biranen kasashe.
Kasashen Afrika ta Kudu, Algeriya da Kamaru ne su ka fi sauran masu fama da cutar a Afrika.