COVID-19: Mun shirya karbar Almajiran asalin jihar Zamfara daga wasu Jihohin – Gwamna Matawalle

0

Gwamna jihar Zamfara Bello Matawalle ya ce gwamnati a shirya take domin yin maraba da almajirai ‘yan asalin jihar Zamfara dake karatun allo a wasu jihohi a kasar nan.

Matawalle ya ce za a yi wa almajiran gwajin cutar COVID-19 a wajen gari kafin a bar su su shiga gari.

“An bude asibitin kula da masu fama da Covid-19 guda biyu a jihar sannan gwamnati ta zuba kayan da za a bukata domin yi wa mutane gwaji da kula da wadanda suka kamu da cutar.

“Gwamnati ta kuma samar da motocin daukan mara lafiya a duk manyan asibitocin dake jihar.

Bayan haka Matawalle ya kara sati biyu akan kwanakin da ya saka na rufe iyakokin jihar.

Ya ce dokar ta hana shiga da fice a jihar amma mutanen dake ciki za su iya tafiya zuwa bangarorin jihar.

” Za mu kama duk motar da ta shiga ko kuma fita daga jihar tare da hukunta duk wanda aka kama a cikin motar.

Matawalle ya ce gwamnati ta dakatar da Tafsiri, sallar Taraweeh da Ittikafi a wannan wata na Ramadan domin hana cunkoson mutane wuri daya.

Ya kuma yi kira ga mutane da su tsaftace muhallin su, wanke hannu da ruwa da sabulu ko kuma a yi amfani da sinadarin tsaftace hannu da yin amfani da takunkumin rufe baki da hanci idan za a fita.

Gwamnati ta ce za ta raba wa mutane abinci domin tallafa wa tallakawa a lokacin Ramadan.

A ranar Juma’a jihar Zamfara ta samu mutum biyu da suka kamu da cutar coronavirus.

Share.

game da Author