COVID-19: Katsina ta dakatar da Sallar tarawiyyi da tafsirin Ramadan, ta saka dokar zaman gida dole

0

Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya sanar da saka dokar zaman Gida dole a Birnin Katsina da kewaye.

Masari ya bayyana cewa dole a dauki wannan mataki a jihar ganin yadda ake ta samun karuwar wadanda suka kamu da cutar coronavirus.

Jihar tana da mutum akalla 9 yanzu da suka kamu da cutar.

Dokar Hana walwala a Birnin bai hada da shagunan sauda kayan abinci da masarufi ba, sannan kuma da shagunan saida magani da bankuna.

Bayan haka kuma gwamnatin jihar ta dakatar da tafsiri watan Ramadan da Sallar tarawiyyi. Ta ce kowa yayi sallah a Gida.

Bayan Katsina da kewaye, an saka irin wannan doka kananan hukumomin Dutsinma da Daura.

Share.

game da Author