A ranar Litini ne Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa kashi 90% na mutanen dake dauke da cutar Covid-19 za su warke a kasar nan.
Ehanire ya fadi haka ne a zaman da kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar Covid-19 ta yi a Abuja.
Ya ce mafi yawan mutane kan mai da hankalin su wajen yawan mutanen dake dauke da cutar ba tare da duba yawan da suka warke ba.
Ya ce a cikin mutum 10, 9 sun warke wanda yake cewa haka bai kamata ya daga wa mutane hankalinsu ba.
Sakamakon binciken da hukumar NCDC ta gabatar ranar Litini ya nuna cewa mutane 665 ne ke dauke da cutar Covid-19 a Najeriya.
Daga ciki 188 sun warke sannan 22 sun mutu.
Mafi yawan mutanen da suka mutu na dauke da wasu cututtuka a jikinsu wanda hakan ya sa suka mutu.
Sakamakon binciken Worldometer ya nuna cewa mutane sama da miliyan biyu ne ke dauke da cutar a duniya.
Daga ciki 169,940 sun mutu sannan 645,164 sun warke a duniya.
Bayan haka Ehanire ya ce Hukumar NCDC na kokarin ganin ta kara yawan mutanen da ake yi wa gwajin cutar daga 1,500 zuwa 3,000 a rana.
Ya ce kara yawan mutanen da ake yi wa gwajin ya taimaka wajen bankado mutanen dake dauke da cutar a kasar nan.
Daga nan kuma Ehanire ya ce daga yanzu za a tilasta killace mutanen da suka shigo kasar nan daga kasashen waje na tsawon kwanaki 14.
Ya ce yin haka zai taimaka wajen hana kara shigowa da Covid-19 cikin kasar nan.
Gwamnati jihohi za su bude asibiti dake da fadin gadaje 300 domin kula da masu fama da cutar a jihohinsu. Sannan za a yi amfani da otel da wasu wuraren domin killace mutanen da suka shigo kasar an daga kasashen waje