COVID-19: Kasashen Australia, Spaniya da Italiya sun yi rage tsawon dokar zaman gida dole

0

Domin farfado da tattalin arzikin kasashen su kasashen Australia, Spaniya da Italiya sun rage tsawon awowin dokar zaman gida dole da aka saka a dalilin barkewar annobar coronavirus.

Wadannan kasashe na daga cikin kasashen Turai da cutar ta yi wa illa matuka.

A kasar Australia mutane 14,000 ne ke dauke da cutar sannan 348 sun mutu.

Shugaban kasar Australia Sebastian Kurz ya bayyana cewa kasar ta yi nasarar rage yaduwar cutar da haka ya sa kasar ta ke kokarin maida hankali wajen ganin harkokin jama’a ada kasuwanci sun fara gudana domin tattalin arzikin kasar ya dawo kamar yadda yake a da.

A ranar Talata kasashen Spaniya da Italiya sun rage tsawon dokar hana walwala da gwamnatin ta saka tun wata daya da ya wuce.

A yanzu haka wasu shaguna a wadannan kasashe sun fara aiki.

Kasar Denmark ta bude makarantun boko domin dalibai su koma makaranta sannan zuwa ranar Lahadi gwamnatin kasar za ta bude wasu bangarorin kasuwanci domin farfado da tattalin arzikin kasar.

Sai dai kuma kasar Faransa ta kara wa’adin kwanakin zaman gida dole zuwa ranar 11 ga watan Mayu.

Shugaban kasar Emmanuel Macron ya ce gwamnati ta yi haka ne domin samun nasarar dakile yaduwar cutar a kasar.

Macron ya ce za a bude makarantun boko da zaran wadannan kwanakin da aka kara sun cika.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kara kara wa’adin kwanakin zaman gida dole a Abuja, Legas da Ogun da Kwanaki 14.

A yanzu dai mutum 343 ne ke dauke da cutar a Najeriya, 10 sun mutu a jihohi 19 da Abuja.

Buhari ya kuma kara yawan mutanen da gwamnati za ta tallafawa yayin da ake zaman gida dole daga 2.6 zuwa 3.6.

Share.

game da Author