COVID-19: Gwamnatin jihar Bauchi ta rufe ofishin UNICEF da WHO a jihar

0

Sakamakon gwajin da aka gudanar wa ma’aikatan UNICEF da WHO dake aiki a jihar Bauchi ya nuna cewa mutum daya ya kamu da cutar coronavirus.

Bincike ya nuna cewa mutum daya din da ya kamu da cutar ya yi tafiya zuwa jihar Kano.

A dalilin haka kuwa gwamnati ta sa a yi wa ofishin feshi tare da rufe ofishin na tsawon kwanaki 14.

kwamishinan kiwon lafiya Aliyu Maigoro ya Sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Lahadi.

Maigoro ya ce ma’aikatan kiwon lafiya sun fara neman duk mutanen da suka yi cudanya da mutumin da ya kamu da cutar a jihar Kano da Bauchi domin a killace su.

Rufe ofishin UNICEF da WHO ya sa mutane yin korafin cewa bai kamata a rufe ofishin ba ganin cewa ko da cutar ta bullo a jihar gwamnati bata saka dokar hana walwala da dokar hana taro a jihar.

Binciken da PREMIUMTIMES ta gudanar ya nuna cewa tun a ranar 23 ga watan Maris ma’aikatan ofishin suka tsagaita zuwa aiki a dalilin bullowar cutar coronavirus a jihar.

Jami’in yada labarai na UNICEF Sam Kaalu ya ce da dama daga cikinsu na aiki ne daga gida.

Idan ba a manta ba a ranar Lahadi ne hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta Sanar cewa mutum 627 ne ke dauke da coronavirus a Najeriya.

NCDC ta ce daga ciki 170 sun warke sannan 21 sun mutu.

Wannan shine karo na farko da aka samu yawan mutane har sama da 80 da suka kamu a Najeriya. Jihohin Barno, Bauchi da Katsina duk sun samu rabon su a sakamakon gwajin da aka fitar ranar Lahadi.

Cutar ta bullo a jihohi 22 kenan a kasar nan.

Share.

game da Author