COVID-19: Gwamnati ba za ta saka dokar ‘Zaman Gida Dole’ a jihar Bauchi ba

0

Gwamna jihar Bauchi Bala Mohammed ya bayyana cewa gwamnati ba za ta saka dokar zaman gida dole ba a jihar a matsayin matakin hana yaduwar cutar coronavirus.

Mohammed ya fadi haka ne ranar Talata bayan ya sanar cewa mutum 8 ne ke dauke da Covid-19 a jihar.

A zaman da kwamitin dakile yaduwar Covid-19 na jihar Bauchi ta yi ranar Talata gwamnati ta yanke shawarar za ta saka dokar kyale mutane su yi walwala na dan wani lokaci a maimakon su zauna a gida.

Gwamna Mohammed ya ce an yi haka ne ganin za a shiga watan Ramadan wanda mutane za su bukaci fita da yin ibada.

“Saka dokar zaman gida dole zai hana mutane yin ibada a watan Ramadan domin mutane za su fita zuwa tafsiri da sallolin da aka Saba yi a watan.

Ya ce gwamnati za ta tattauna da al’umar musulmai, Jamaatul Nasirul Islam, sarakunan da masu ruwa da tsaki domin ganin dokar da za a saka a jihar bai shafi ayyukan ibada a jihar ba.

Mohammed ya cewa gwamnati za ta yi kokarin hana yaduwar cutar.

Idan ba a manta ba a ranar 20 ga watan Afrilu ne gwamnati jihar Bauchi ta rufe ofishin UNICEF da WHO bayan an gano wani ma’aikacin wurin ya kamu da coronavirus.

Za a rufe ofishin na tsawon kwanaki 14 bayan an yi feshi a wurin.

Share.

game da Author