Tun bayan bullar cutar coronavirus mai sarke numfashi a Najeriya a cikin watan Fabrairu, jihohi suka fara daunkan matakan kariya ga al’umman su.
Da farko dai jihohin Arewa maso yamma sunyi taro na gwamnoni inda suka yanke shawarar rufe makarantu Na tsawon kwanaki talatin, don dakile yaduwar cutar tun ma kafin ta shigo jihohin.
Kowa ya sani a Arewacin Najeriya, jihar Kano da Kaduna sune ginshikai kuma abin dubi da kallo ga saura. Kuma duk abinda ya shafe daya daga ciki ba karamar tasiri zai yi ba ga sauran, dama Najeriya baki daya.
Wannan ka iya zamantowa dalilin da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru ya hanzarta daukar wasu kwararan matakan kariya da dakile cutar ko da ta iso jihar fiye da wadanda cutar ya ishe musu, duk da bai ma wasu al’umma dadi ba.
Amma cike da mamaki, jama’a na ta maganganu kan yadda tun farko a fili gwamnatin Kano bata dauki muhimman matakai na kariya da hana shigowar wanna mummunar cuta jihar, wacce ta ke ta biyu a yawan jama’a a fadin Najeriya kuma da daya a Arewa.
Daga baya jihar ta hana shige da fice, Wanda majiyoyi ke nuni da cewa bata wani yi tasiri ba. Wannan kuwa na iya alakantuwa da yanayi na neman abinci da jama’a ke fita yi.
A ranar 11 ga watan Afrilu jihar Kano ta fara samun mai dauke da cutar COVID-19 a jihar, wanda rahotanni ke nuni da cewa wani tsohon jakadan Najeriya ne a kasan waje. Abin haushi shine yadda mutumin ya boye tarihin ciwon da kuma tafiye-tafiye da yayi a lokacin da likitan da ya fara duba shi ya tambaye shi. Wannan bawan Allah dai an gano ya zo daga kasar waje kuma ya tsaya Abuja inda aka mai gwajin COVID-19, ya wuto Kaduna da kuma Kano, amma ya boye cewar hakan. Wanda yake abin Allah wadai ne ga duk wani dan adam yayi haka balle mai ilimi kamar jakada.
Cikin kwanaki kadan kuwa, mutane a Kano da suka kamu da cutar har ya kai 21 fiye da na sauran jihohin Arewaci Najeriya, kuma mutum daya da ya rasu. Wannan ka iya faruwa ne saboda rikon wasa da akai mata a Kano har ta yadu haka.
Wannan dai abin firgitar wa ne ganin yadda jihar ke dauke da jama’a a gwamutse, wanda ka iya sa tai saurin yaduwa. Bugu da Kari, akwai harsashen mutane da yawa a dauki da cutar amma basu sa ni ba, ko kuma sun sani amma sunki zuwa a gwada su.
Bisa ga wadannan, ya kamata jihar Kano ta dau kwararan matakai kamar:
1. Karfafa dokar hana fita kamar yadda wasu jihohi suka yi. Kamar a yau jama’a akwai videos da ke nuna masallatai sun yi sallar jama’a,wanda wannan gangaci ne.A kwai kuma rahoton kama limamin wani masallaci wanda yayi daidai.wannan ka iya nuna cewa limamin na da karanci ko gurguwar fahimtar cutar covid 19 da kuma karantar wa islama a yanayi annoba.
2. Fito da ingantacciyar tsari cikin sauri domin ciyar da mabukata don gudun karya dokar fita. Dama in kaga amutum a waje, neman abinci yayje, toh in an bashi zai zauna a gida. A cire siyasar a taimaka wa mabukaci!
3. Kokarin yin gwajin cutar ta hanyar bin lunguna dai dai gwargwado in har da kayan hakan.
4. Karfafa wayar da kan al’umma ta hanyoyi mabanbanta .tare da amfani da Sarakuna da malaman addini da kungiyoyi da sauransu.
Ya Khadimul Islam ta farga ka tashi haikan ka taimaka kan ka, da al’ummar jihar ka da Arewa da Najeriya baki daya. A Arewa dai Yanzu duk hankali ya koma jihar ka don gani yadda cutar take ta Kara yaduwa cikin kwanakin kadan. Ka sani ciwon dan yatsar Kano tamkar zazzabi ne ga sauran jihohi.
Allah ka tsare mu, Amin.
Khadijah Sulaiman. Malama a tsangayar koyar da aikin Jarida a kwalejin kimiyya da fasaha dake zariya.
Khadijahsulaiman93@gmail.com