COVID-19 GASKIYA CE: Anya gwamnatin jihar Jigawa da gaske take wajen yaki da cutar? Daga Adamu Saleh

0

Hakika lokuta dayawa kokarin Gwamnati na fitowa fili, mukan gani a kasa, mun gode. Jaka zalika Muna Kira kan akwai abubuwan dake faruwa daya kamata a duba su da wuri don samun mafita kafin matsala ta fado ciki. Cutar coronavirus (covid 19) na yunkurin ta’azzara a kasarmu dai dai lokacin da duniya ta rude ta kidema ta kasa hango mafita domin rashin takamaiman mafita. Kasuwanci, wasanni, tattalin arziki, gwamnati duk komai ya tsaya cak sanadiyyar wannan cuta data gagari duniya lokaci daya.

Jihar Jigawa tayi makwabtaka da Kano, Katsina, Bauchi, Yobe da Jamhuriyar Nijar. Banda Yobe duka makwabtan mu nada wannan cutar hasali ma muma munada wanda ya kamu da ita guda daya. Abunda ke faruwa a Kano fa na tunatar da jihohin dake makwabtaka da ita cewar fa matsala na nan tafe matukar ba’ayi hattara ba, dole ne mu nutsu sosai da sosai wajen samowa al’ummar mafita kafin abun yafi karfinmu ta kowace irin hanya.
Saboda haka muna Kira ga Gwamnati ta duba abubuwa kamar haka:

1. ‘Team’ daya ne yake aiki tare da yawo a duk lokacin akace an samu wani dake zaton ya kamu da cutar a fadin jihar sannan kuma jihar Jigawa nada kananan hukumomi har 27 kuma akwae nisa mai yawa tsakanin wasu LGs. Yakamata a kara yawan teams din yakai biyar yadda kowace masarauta nada nata team din.

2. Wajen gwaji wato (testing center) ganin yadda cutar ke ta yaduwa akwai bukatar Jigawa itama ta nemi gwamnatin tarayya da a kafa ‘center’ daza a rika yin gwaji mai makon kaiwa Abuja tunda kayan aikin Kano sun kare kuma ba’a kawo ba, kaga bazai yiwu ba ana aiki da tsayawa a irin wannan aikin.

3. Kayan amfani da masu duba marasa lafiyar zasu na amfani dasu lokacin gudanar da aikinsu wanda akafi sani (Personal Protections Equipment) wato PPE. Rashin wannan kayan ya jefa likitoci da masu aikin lafiya cikin hatsari mai tarin yawa domin yanzu sai kamuwa suke da cutar a Kano da Lagos da ma wasu jihohin dai dai lokacin da suke yakar cutar. Yakamata a samar da PPE masu yawa bawai a manyan asibitoci kawai ba, har kanana dake kauyuka.

4. Mun ga masara da aka saba rabawa yan siyasar gwamna a kowane watan azumi, wannan lokacin yace a rabawa talakkawa, mun gode. Muna roko da a duba yanayin Kazaure da tashi na Lockdown a kawo mata dauki na gaggawa kamar yadda muke ji yana faruwa a Wasu jihohin.

Mai girma gwabna hakki ne ya rataya a wuyakanka kasancewar ka wanda jama’a suka zaba domin tafi da harkokinsu a kowane irin yanayi, yakamata ka kara tashi tsaye da zage damtse wurin kare masu lafiyar su da tsaronsu gaba daya.

Allah kare mu daga wannan annoba gaba daya. Allah taimaki Jihar Jigawa abun alfaharinmu ameen.

Adamu Saleh Maidalibai, dalibi a jami’ar Bayero dake Kano.

Share.

game da Author