COVID-19: Bauchi ta rufe makarantun allo, ta saka dokar ‘Zaman Gida Dole’

0

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da rufe duka makarantun allo dake fadin jihar domin dakile yaduwar cutar Covid-19 a jihar.

Gwamnan jihar Bala Muhammed ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis.

Almajiran dake makarantun allo na shiga cikin mutane don rokon abin da za su ci sannan da dadare su cunkusu wuri daya su yi barci.

Haka da suke yi na iya yadda cutar a jihar wanda dole ya sa gwamnati ta rufe makarantun domin kare mutane daga kamuwa da cutar.

Mohammed ya kuma ce gwamnati ta kammala shiri tsaf domin karbar almajirai ‘yan asalin jihar dake karatu a wasu jihohi a kasar nan.

Ya ce za a killace almajiran da suka dawo jihar daga wasu jihohin a sansanin ‘yan butan kasa dake Wailo domin danka kowane yaro ga iyayensa.

“Duk gwamnonin Arewa sun amince su dawo da almajirai jihohin su na asali.

“Gwamnati ta kammala shirin domin komar da almajiran dake jihar Bauchi jihohin su na asali.

Bayan haka Muhammed ya ce gwamnati ta saka dokar zaman gida dole a jihar. Ya kuma ce gwamnati ta hana taron mutane musamman na addini a jihar.

Mohammed ya ce dokar zata fara aiki daga ranar Lahadi 26 ga watan Afrilu.

Daga ranar 26 ga watan Afrilu ba za a bude masallatai, coco-coci da kasuwanin a jihar ba. Sai wadanda suke saida abinci a duk ranakun Litini, Laraba da Asabar. Sannan Kuma gwamnati ta hana yin kabu-kabu na Achaba a jihar sai Keke-Napep kuma mutane biyu kacal za su rika dauka.

Sannan kuma gwamnati ta dauki nauyin saka tafsiri a talabijin da radiyo domin mutane su rika saurare a gidajen su. Domin an dakatar da haka a wannan wata.

Idan ba a manta ba a ranar 22 ga watan Afrilu ne Mohammed ya bayyana cewa gwamnati ba za ta saka dokar zaman gida dole ba a jihar a matsayin matakin hana yaduwar cutar coronavirus.

Share.

game da Author