COVID-19: Babu tabbacin rigakafin BCG na maganin cutar – WHO

0

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa babu sahihan bayanin da ya nuna cewa allurar rigakafin BCG na samar da kariya ko kuma warkar da cutar coronavirus a jikin mutum.

Allurar rigakafin BCG rigakafi ne da ake yi wa jarirai da yara kanana domin kare su daga kamuwa da cutar tarin fuka.

WHO ta fadi haka ne bayan wasu masu gudanar da bincike dake makarantar Johns Hopkins Bloomberg a kasar Amurka sun bayyana sakamakon binciken su da suka nuna cewa kasashen duniya dake amfani da allurar rigakafin BCG na samun kariya daga coronavirus.

Sakamakon binciken ya kuma nuna cewa coronavirus bata kashe mutane da yawa a kasashen dake amfani da rigakafin BCG.

WHO ta ce har yanzu babu maganin cutar coronavirus sannan bata da tabbacin cewa rigakafin BCG da ake yi wa yara na samar da kariya daga kamuwa da cutar.

Kungiyar ta ce za ta gudanar da bincke domin gano gaskiyar wannan lamarin.

WHO ta kuma yi kira ga kasashen duniya da su ci gaba da yi wa yara allurar rigakafin BCG domin kare su daga kamuwa da cutar tarin fuka.

A cikin makon da ya gabata ne PREMIUM TIMES ta buga bayanin cewa Cutar Coronavirus ta kama fiye da mutum milyan 1 a duniya, sama da 50,000 sun mutu.

Sannan sama da mutum 500 sun mutu dalilin Coronavirus a Afrika, yayin da wasu 900 suka warke daga cutar.

A Najeriya cutar ta yadu zuwa jihohi 19 da Abuja sannan mutum 343 ne ke dauke da cutar a kasan.

An sallami 91 sannan mutum 10 sun mutu.

Share.

game da Author