A ranar Laraba ne ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Legas ta bayyana cewa an sallami mutum 49 da suka warke daga cutar Covid-19 a jihar.
Ma’aikatar ta ce an sallami wadannan mutane ne bayan sakamakon gwajin da aka yi musu sau biyu ya nuna cutar ta fice daga jikin su.
Daga cikin mutum 49 din da aka sallama akwai mata 28, maza 21.
Wannan shine karo na farko da jihar za ta sallami mutum har 49 a rana daya.
Zuwa yanzu jihar ta sallami mutum 187 da suka warke daga cutar.
Bisa ga sakamakon gwajin da Hukumar NCDC ta fita ranar Talata ya nuna cewa mutum 860 ne ke dauke da cutar a jihar Legas.
Daga ciki an sallami 187 sannan 19 sun mutu.
Mutum 1532 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 255 sun warke, 44 sun mutu.
Idan ba a manta ba a ranar Talata ne Hukumar NCDC ta bayyana cewa Najeriya na cikin matsanancin fama da karancin kayan gwajin masu dauke da cutar Coronavirus.
NCDC ta ce akwai matukar karancin kayan gwaji, wadanda ya ce ana bukatar karin masu yawan gaske domin a yawaita gwajin da ake yi a kowace rana a kasar nan baki daya.
Hukumar ta fadi haka ne lokacin da ake korafin cewa Najeriya ba ta tabuka abin kirki idan aka yi la’akari da yawan wadanda ta yi wa gwaji a kasar nan.
Kasashe da yawa wadanda ba su kai yawa da karfin Najeriya ba, irin su Ghana da Afrika ta Kudu, sun yi wa mutane da dama fiye da Najeriya gwaji.