COVID-19: An killace matafiya 600 a jihar Filato

0

Gwamnatin jihar Filato ta killace wasu matafiya 600 da suka shigo jihar.

Kwamishinan kiwon lafiyar jihar Lar Ndam, ya Sanar da haka da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Laraba a garin Pankshin.

Ndam ya koka kan yadda wasu ‘yan jihar dake zama a wasu jihohi a kasar nan ke karya dokar hana shiga da fice da gwamnati ta saka “Gwamnati ta saka wannan doka ne domin hana yaduwar cutar coronavirus wanda da taimakon Allah har yanzu cutar ba ta bullo a jihar ba.

“Mun killace mutum 49 a wurin shakatawa na Godiya Resort, mutum 545 na killace a sansanin ‘yan bautar kasa dake Jakatai a karamar Hukumar Mangu.

“Ya zama dole gwamnati ta dauki tsauraran matakai wajen ganin mutane basu karya dokar shigowa jihar Filato daga wasu jihohin.

Bayan haka shugaban jami’an tsaro dake Pankshin Sam Mbok ya bayyana cewa sun killace mutane 12 da suka karya dokar hana shiga da fice da gwamnati ta saka.

Mbok ya ce sun kama mutanen ne ranar 21 ga watan Afrilu sannan suna killace a sansanin masu butane kasa.

“Daga cikin mutane12, biyar sun fito daga jihar Kano, wasu biyar daga jihar Abia, daya daga Niger sannan daya daga jihar Legas.

Ya kuma ce jami’an tsoron sun kara kama wasu mutum hudu a garin Mangu wanda a yanzu haka suna killace a sansanin masu butane kasa a karamar hukumar Mangu.

Kwamishina Ndam ya yi kira ga Jami’ar tsaron da su kara zage damtse wajen ganin sun hana mutane karya dokar da gwamnati ta saka.

Ya kuma yi kira ga sarakunan da sauran mutane da su sanar da jami’an tsaro a duk lokacin da baki suka shigo yankinsu.

Idan ba a manta ba Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Talata.

A bayanan da NCDC ta fitar ranar Talata, Legas ta samu karin mutum 59, Abuja 29, Kano 14, Katsina 3, Ogun 3, Bauchi 1, Barno 6, Ribas 1.

Yanzu mutum 782 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 197 sun warke, 25 sun mutu.

Share.

game da Author