COVID-19: An killace matafiya 200 a jihar Nassarawa

0

Gwamnatin jihar Nasarawa ta killace matafiya sama da 200 da suka shigo jihar daga jihohin da cutar Covid-19 ta yadu.

Antoni -Janar, kuma kwamishinan shari’a wanda shine shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar Covid-19 na jihar Abdulkarim Kana, ya fadi haka a zaman da kwamitin ta yi ranar Talata a garin Lafia.

Kana ya ce an tsare matafiyan ne a daidai suna kokarin shigowa wanda yin haka saba wa dokar gwamnatin jihar ne na hana baki shigowa jihar.

Ya ce gwamnati ta killace matafiyan har na tsawon kwanaki 14 sannan ta dibi jinin su domin a yi musu gwajin cutar.

“Sakamakon gwajin wasu daga cikin su ya fito inda ya nuna cewa ba su dauke da cutar sannan har an sake su.

Bayan haka kwamishinan ‘yan sanda Bola Longe ya ce Jami’ar tsoro sun kama mutane sama da 400 a dalilin karya dokar zaman gida dole da gwamnati ta kafa.

Longe ya yi kira ga mutane da su kiyaye duk dokokin da gwamnati ta saka cewa Jami’ar tsaro ba Za su yi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wanda ya karya doka a jihar.

Kwamishinan yada labarai Dogo Shammah ya ce gwamnati za ta raba abinci domin rage wa mutane zafi yayin da suke zama a gida.
Shammah ya ce gwamnati za ta ci gaba da ba da bayanai game da cutar da matakan hana yaduwar cutar da gwamnati ta dauka domin dakile cutar a jihar.

Gwamnan jihar Abdullahi Sule ya ce mutum daya ya kamu da cutar a jihar.

Sule ya ce an gano cutar ne a jikin wata mata mai shekaru 25 da ta kamo hanya daga jihar Kano zuwa Lauren Garaku dake karamar hukumar Kokona a jihar,Nasarawa.

Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Talata.

Yanzu mutum 1532 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 255 sun warke, 44 sun mutu.

Share.

game da Author