COVID-19: Allah yayi wa Abba Kyari rasuwa

0

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Kasa Abba Kyari ya rasu a dalilin fama da yayi da cutar coronavirus.

Maitaimaka wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya bayyana haka a madadin gwamnatin Tarayya.

Adesina ya ce Abba Kyari ya rasu ranar Juma’a a asibiti a Legas.

Kuma za a bayyana ranar da za a yi jana’izar sa nan ba da dadewa ba.

Idan ba a manta ba a ranar 29 ga watan Maris, Abba Kyari ya sanar da cewa za a maida shi asibiti a Legas domin a ci gaba da duba shi.

Sai dai ko a lokacin bai fadi ko wani asibiti bane za a kwantar dashi.

PREMIUM TIMES ta gano wani asibiti mai zaman kan sa dake Ikoyi a Legas aka kwantar da Marigayi Abba Kyari.

Majiya mai karfi daga asibitin ya shaida wa jaridar cewa Marigayi Abba Kyari yayi fama da wannan cuta tun bayan da aka kwantar dashi a asibitin.

Majiyar ya ce, a wasu lokuttan ma har wasu manyan asibitoci aka rika Kai shi ana yi masa gwaje-gwaje.

Ranar Juma’a, hukumar NCDC ta bayyana rasuwar wasu mutum hudu daga cutar coronavirus da bata da magani har yanzu ana gani ciki har da marigayi Abba Kyari.

Sannan kuma mutum sama da 490 suka kamu da cutar a Najeriya.

Jihar Kano da bata wuce mako daya da bayyana mutum na farko da ya kamu da cutar ba ta zarce jihohin kasarnan a yawan wadanda suka kamu.

Yanzu ita ce jiha ta uku dake da yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya bayan Legas dake da mutum sama da 200 kwance.

Share.

game da Author