Gaskiya bana goyon bayan attajirai wadanda suka zirawa gwamnati ido a wannan lokacin da talakawa suke matikar bukatarsu. Bayan kudade da wasu daga ciki suka bawa gwamnati don yaki da annobar a Najeriya, akwai bukatar yin gidauniya kala kala don taimakawa wadanda idan aka barsu suka yi kwana uku a gida babu tallafi zasu iya shiga wani hali.
Misali, a jihohin da nafi sani, sune na Arewacin Najeriya. Allah ya albarkancemu da attajirai masu kudin gaske irinsu Alhaji Aliko Dangote Kano wanda yafi kowa kudi ma a nahiyar Afrika, Alhaji Abdussamad Rabiu Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata Kano, Hajiya Mariya Sunusu Dantata Kano, A.A Rano Kano, Alhaji Dahiru Mangal Katsina, T.Y Danjuma Taraba, Alhaji Atiku Abubakar Adamawa da sauransu. Wadannan fa kadan ne daga cikinsu muka bayyana saboda su kansu gwamnati ne. Sannan duniya ta yadda cewa sune attajiran kasarmu. Banda matasan masu kudi na kasar.
Muna yi musu fatan alheri, Allah ya kara musu arziki, kuma muna alfahari da godiya ga wasu daga cikinsu, musamman wadanda suka dauki kudi masu yawa suka bawa gwamnati don yaki da annobar COVID-19. Saidai shi talaka yana bukatar ganin tasirinsu a kwanon tuwonsa. Gaskiya haka muka ga ana yi a kasashen da annobar ta fara dasu. Bayan attajirai sun taimakawa gwamnati sai muka ga suna hada asusun tallafawa talakawa. Wannan arziki ne sosai.
Saboda ita fa dukiya amfaninta ga mutum shine yin amfani da ita wajen taimako a lokacin da ya dace, idan ba haka ba babu wata rana da zata yi maka a lahira. Annabi (SAW) yace, a ranar lahira, dinar baya amfani saidai lada ko zunubi, da su ake amfani wajen biyan bashi. Allah ya kaimu lafiya.
Idan ma hujjojin musulunci basu gamsar da wadanda ba musulmi ba, to wani dan gurguzu mai suna Karl Marx yace, a cikin nazarinsa akan “Class struggle and conflict”, dole ne a dinga samun rashin zaman lafiya tsakanin masu kudi da talakawa saboda takara suke yi wajen mallakar junansu. Me kudi yana so ya kara find talaka, shima talaka yana son yi masa juyin mulki. To mu a musulunci, Annabi (SAW) yace, alheri da kyautatawa suna karawa mutum farin jini a cikin al’umma.
Duk mutumin da yake da imani, duk matsayin jari-hujjar mutum zai tausayawa faqirai a wannan lokacin. Shine amfaninka ga talakawa kuma hakan ne zai sa su dinga yi maka fatan alheri. Amma saidai abun mamaki duk tarin dukiyar wasu mutanen sun koma gefe sun zirawa talakawa ido. Wallahi dole talakawan su dinga jin haushinsu. Saboda Annabi (SAW) yace, dukiyar da mutane suke morarta sun fi yi mata fatan alheri.
Allah ya karemu, talakawa ku daure ku bi doka ku zauna a gidajenku don Allah.