Yawan maganganu akan annobar coronavirus a gaban iyayenmu dattijai wadanda suke fama da cutar hawan jini ko ciwon siga bai kamata ba. Hakan yana tasiri matika wajen hargitsa su sosai.
Duk mutumin da yake da shekaru, musamman idan yana da hawan jini, kamata yayi a dinga 6oye masa duk wani abu da zai iya tayar masa da ciwon. Misali, yawan alakantar da cutar coronavirus da kashe tsofaffi yana da tasiri wajen hargitsa mana su.
Gaskiya ko radiyo da TV ayi kokari a rika rage yawan sauraronsu a gaban iyayenmu da suke da ciwon damuwa. Balle kuma ka dinga nunawa ko baiwa iyayenka labarin abubuwa masu tayar da hankali a wayarka akan wannan annoba.
Tabbas, wannan yana cikin abubuwan da suke ta6a lafiyar dattijan da suke mutuwa a Kano. Ban ce babu wasu dalilan ba, akwaisu sosai, amma zaka iya gwada wannan maganar tawa a gidanku idan iyayenka suna raye. Saboda mafi yawancinmu bama kula da labarin da ya dace mu fadawa dattijan da muke dasu.
Abu ne mai kyau a dinga kwantar musu da hankali ta hanyar tuna musu Allah, tunda galibi iyayen namu bayin Allah ne masu tawakalli. Har yanzu duniya bata buga kansu ba kamar mu. Mutuwa lokaci ce, babu tsoho babu yaro, duk wanda Allah ya kira dole ya amsa kiran.
Sannan a cikin wannan yanayin a kula sosai da irin maganin da iyayenmu suke amfani dasu. Sannan a dinga tsayawa a kan su don a tabbatar suna sha. Kada a barsu maganin da likita ya dorasu akai ya yanke musu idan har da hali saboda asibiti yanzu ba lallai bane a samu yadda ake so. Hankalin likitoci ya koma kan coronavirus.
Allah ya rabamu da iyayenmu lafiya ya kuma karemu daga wannan annoba
Discussion about this post