Shugaban Amurka Donald Trump, ya nuna firgicin cewa nan da makonni biyu annobar Coronavirus za ta kara kashe dimbin Amurkawa.
Ya ce annobar ta yi muni sosai a kasar, ta yadda daga yau din nan kasar za ta kara tsunduma cikin mummunan halin yawan mace-macen dubban jama’a da za a fuskanta daga nan zuwa cikin makonni biyu masu zuwa.
Sai dai kuma ya karyata zargin da ‘yan jaridu suka yi masa na kin wadatar da jihohi da na’urorin shakar numfashi da hana numfashi daukewa, wato ventilators
Ya ce wasu gwamnonin sun rika neman fiye da yadda yadda yadda kamata su nema. Hakan ne ya ce ya sa aka rika tunanin kamar ba a wadatar da su din ba.
Coronavirus ta kashe sama da mutum 8,300 a Amurka, sannan ta kama sama da mutum 306,000. Har yanzu cutar ta fi yin mummunar illa a jihar New York.
Masana kiwon ladiya a Fadar Shugaban Kasa ta White House ta yi kintacen cewa kafin a shawol kan cutar a Amurka, mai yiwuwa ta kara kashe mutum 100,000 zuwa 240,000 nan da kwanaki kadan masu zuwa.
“Rabon Amurka da ta ga irin wannan bala’i watakila run Yakin Duniya na Farko ko na Biyu.”
Coronavirus ta kashe kusan mutum 60,000 a duniya.
Ta fi yin mummunar illa Amurka, Spain, Italy da Chana.
Har yanzu dai ba ta yi wa Afrika rubdugu ba kamar yadda ta yi wa kasashen Turai da Amurka da Asiya.
Annobar ta tsaida komai cak a duniya, inda farashin danyen mai ya fadi warwas sannan ya haddasa durkushewar tattalin arziki.