Coronavirus: Za a killace wadanda suka halarci jana’izar Abba Kyari

0

Mahukunta a babban birnin Tarayya sun shaida cewa za a killace wasu da suka halarci jana’izan marigayi Abba Kyari da aka yi a Abuja ranar Asabar.

Sakataren Lafiya na Abuja, Mohammed Kawu, ya bayyana cewa za akillace duka ma’aikatan makabartar, sannan za ayi musu gwajin cutar coronavirus.

Sannan kuma akwai wasu har 11 da za yi wa wannan gwaji a dalilin cudanya da juna da suka rika yi a makabarta.

Wani babban ma’aikacin FCT ya shaida wa PREMIUM TIMES, cewa lallai an samu matsala a makabarta wajen bizne marigayi Abba Kyari, domin ba irin shirin da ya kamata ayi aka yi ba. Ya koka kan yadda aka kyale mutane suka halarci wurin sannan aka yi ta cudanya da juna.

Ya tabbatar cewa an tsamo wasu mutane 11 daga cikin wadanda suka yi cudanya a wannan wuri domin yi musu gwajin cutar.

Bayan haka ya roki mutane su kwantar da hankalin su, cewa gwamnati za ta bi diddigin abin domin kada a samu yaduwar cutar.

An yi ta nuna wani bidiyo da aka dauka na wani da ya halarci jana’izar yana cire kayan kariya da ya saka a bayan katangar makabartar ba tare da jami’an lafiya sun taimaka masa ba.

Ya cire kayan ya saka a cin wani jan leda, ya jefar da ita a gefen makabartar. Sai dai mahukunta sun ce tun bayan bayyanar wannan bidiyo suka garzaya wajen aka dauke wannan leda sannan kuma ana bin su gida-gida domin a killace da yi musu gwaji.

Abba Kyari, ya rasu ranar Juma’a a Legas bayan fama da yayi da cutar coronavirus.

Share.

game da Author