Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar cewa ta ta damke wasu matasa har 30 a dalilin buka kwallon kafa da suka yi a fili bayan an saka dokar zaman gida dole a jihar.
Kakakin yan sandan Jihar Abdullahi Haruna ya bayyana cewa, wadannan matasa dake zaune a karamar hukumar Dala, sun bijirewa umarnin gwamnati ne inda suka shirya wasan kwallon kafa a tsakanin su a wannan lokaci da aka saka dokar hana walwala don coronavirus.
Bayan haka kuma yace yara da matasa sukan fito kan tituna suna buga kwallon kafa a jihar. Ya gargade su cewa duk wanda aka kama zai kuka da kan sa.
” Sannan wadannan da muka damke su za a garzaya da su ofishin masu aikata laifuka domin a zartar musu da hukuncin karya doka da suka yi.
Wani malamin makarant mai suna Abubakar Nuru, ya yi kira ga iyaye da su rika kwaban ya’yan su, a hana su karya doka sannan su rika tsare su a gida.
Shima Kabiru danlami wadda malamin lafiya ne ya ce iyaye ne ke dawo wa gwamnati da hannun agogo baya, domin basu tsawata wa ‘ya’yan su.
Jihar Ko wacce daga baya-bayannan ta samu mutum na farko da ya kamu da coronavirus, yanzu tana kan gaba waje yawan wadanda suka kamu da cutar. Ita ce jiha ta uku a yawan wadanda suka kamu.