CORONAVIRUS: ‘Yan jarida na saida rai kamar yadda jami’an lafiya ke yi -Lai Mohammed

0

Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, ya ce ‘yan jarida masu bibiyar yadda ake tafiyar da ayyukan yaki da Coronavirus, su na cikin hatsarin yiwuwar kamuwa da cutar, kamar yadda jami’an lafiya masu kula da masu fama da cutar ke cikin hatsarin kamuwa su ma.

Lai ya ce dole a kalli gudummawar da ‘yan jaridar ke bayarwa a yaki da dakile Coronavirus, tamkar wasu zaratan sojoji ne a fagen yaki.

“Ba don irin gagarimar gudummawar da ‘yan jarida ke bayarwa ba, ba za a cimma nasarar da ake son a cimma ba.”

Lai ya yi wannan jawabin a lokacin da ya ke amsa tambayoyi wurin taron manema labarai masu bibiyar irin ci gaba da ake samu a kullum a Kwamitin Yaki da Annobar Coronavirus a Najeriya.

“Har yanzu babu maganin cutar Coronavirus a duniya. Abu daya da ake yi domin kauce wa kamuwa da cutar, shi ne amfani da kafafen yada labarai ana ilmantar da jama’a irin matakan da za su rika dauka domin kada su kamu da cutar.

“Mu na fata kuma mu na addu’a Allah ya kare ku da ga wannan cuta. Amma irin yadda ‘yan jarida a kasar nan da duniya ke bibiyar dauko labaran wadanda suka kamu da cutar Coronavirus, su ma su na cikin hatsarin yiwuwar kamuwa.

“Ya kamata mu bibiyi gidajen jaridun da ku ke wakilta domin mu ga irin tsarin inshorar da suka tanadar wa masu dauko musu labaran cutar Coronavirus.” Inji Lai Mohammed.

Share.

game da Author