Tawagar Ceto Al’ummar Kano daga Coronavirus da Shugaba Muhammadu Buhari ya tura, tuni ta dira Kano kuma ta kama aikin da ya kai ta.
Da isa birnin daidai lokacin da ake cikin zazzafan fargabar fantsamar cutar, biyo bayan ganin yadda mutane birjik ke mutuwa a birnin mafi girma da yawa a Arewacin Najeriya.
Dirar su ke da wuya suka zarce Gidan Gwamnatin Jihar, inda shugaban tawagar Nasiru Gwarzo, wanda dan Kano ne, ya shaida wa Gwamna Abdullahi Ganduje ce Shugaba Muhammadu Buhari ya turo su, domin su ga halin da jihar ke ciki kuma su binciki abin da Kano ke bukata wajen yaki da cutar Coronavirus.
“Mai Girma Gwamna, Shugaban Kasa ya turo my ne domin mu zo mu tabbatar da mun yi duk wani bakin kpkarin domin mu tsaida fantsamar Coronavirus a jihar Kano. Ya ce mu yi aiki da ko da wasu kafafe ne daga wajen Najeriya da kuma aiki tare da gwamnatin jiha domin samun wannan nasara.
Ya sanar da gwamna cewa tare da shi akwai kwsrarrun jami’an kiwon lafiya, likitoci da masana kwayoyin cututtuka.
“Ba wai mun zo ne da wani sabon abu ba. Mun zo ne domin mu tilasta cewa lallai ana aiki da matakan da muka taras gwamnatin Kano ma amfani da su ka’in da na’in.”
Ganduje ce a bayyana masa cewa sun zo a daidai lokacin da yq dace kuma a lokacin da ake tsananin Bukatar su.
“Shugaba Buhari ya yi tunanin mai kyau da ya turo ku, domin zuwan na ku zai ba Ku damar ganin wurare da banharen da ya kamata a inganta wajen yaki da cutar Coronavirus.”
Ganduje ya yi amfani da damar ya kara jaddada kiran da ya yi a baya, inda ya roki a kara wuraren gwajin cutar Coronavirus a Kano.
“Samar da wuraren na da matukar muhimmanci a yaki da annobar Coronavirus. Domin shi ne zuciyar yaki da cutar. Za mu ba Ku cikakken hadin kai, tunda dama tuni mu ke jiran isowar ku.”
A na sa jawabin, Shugaban Hukumar NCDC na farko, Abdulsalam Nasidi, ya ce ba sun je Kano ba ne don su rushe wani tsari da aka rigaya aka yi a jihar, sun je ne domin su karfafa kuma su tilasta yin aiki yadda ya kamata domin a cimma nasarar dakile Coronavirus a Kano.