Akalla gwamnonin Najeriya shida ne suka wancakalar da dokar hana taro a jihohin su suka ba mutane daman a cakude kawai duk da dokar hana haka da gwamnatin tarayya saka kuma tayi kira a kan abi.
Gwamnonin Najeriya sun ba mutane dama su ci gaba da halartar wuraren bautar su da yana da coci-coci da masallatai domin yin ibada ba tare da la’akari da coronavirus da gwamnati ke kokawa da ba a kasar nan da fadin duniya.
Babban hanyar da ake iya dakile yaduwar cutar coronavirus shine kaurace wa gungun jama’a. Idan aka yi haka za a rage yada cutar.
A hira da NTA ta yi da ministan yada labarai, Lai Mohammed, ya roki gwamnonin jihohi da su daina maida da yaki da cutar coronavirus da Najeriya ke yi siyasa.
Jihohin Katsina, Ribas, Kogi, Ondo, Bayelsa, Ebonyi duk sun sawwaka wa mutane su rika fita zuwa wuraren Ibada musamman a wannan lokaci na bukin Easther.
A jihar Katsina, gwamnan jihar Aminu Masari, ya amince wa musulmai su rika fita sallan Juma’a sai dai a rika takaita huduba. Duk da cewa a kasashen musulmai na duniya duk an dakatar da haka saboda illar wannan cuta.
A jihar Ribas, Gwamna Nyesom Wike, ya amince musulmai su yi sallan Juma’a, suma kiristoci su wataya a wajen bukin Easther su garzaya coci komai yawan su su yi ibada.
A Jihar Ebonyi, Gwamnan jihar ya ba mutanen jihar daman su je su bizine mamatansu, daga ranar 9 zuwa 20 ga watan Afrilu.
Shi kuma Akeredolu na jihar Ondo ya ce mutanen jihar za su iya garzayawa coci domin ibadan bauta ta Easther a karshen wannan mako.
A jihar Bayelsa kuma gwamna Douye Diri, ya ce gwamnati ta saussauta dokar ne domin mutane a shigo da abinci daga iyakokin jihar dake datse ada.
Shima gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya wancakalar da wannan doka inda ya umarci duka mabiya addinai a jihar su rika halartar wuraren ibadan su a duk lokacin yin haka.