CORONAVIRUS: Yadda aka hana manyan hadiman Buhari shiga Aso Rock bayan halartar jana’izar marigayi Abba Kyari

0

Kakakin fadar shugaban Kasa ya bayyana cewa ba laifi bane hanasu shiga fadar gwamnati bayan sun dawo daga jana’izar marigayi Abb Kyari.

Garba shehu ya ce hakan na daga cikin dokokin ma’aikatar lafiya domin hana yaduwara cutar coronavirus.

Manyan jami’an gwamnati sun karya dokar hana cakudar jama’a na gwamnati inda suka dunguma zuwa makabarta wajen jana’aizan Abba Kyari. Hakan da suka yi ya sa ana zargin akwai yiwuwar cutar ta kama wasu daga cikin su.

Shugaban kasa ya yi matukar nuna rashin jin dadin sa game da yadda hadiman sa suka karya dokar nesa-nesa da juna suka garwaya kansu a wajen jana’izar marigayi Abba Kyari.

Saharareporters ta ruwaito cewa dukkan su sun hadu da jami’ai a kofar shiga fadar gwamnati inda suka kora su duka suka ce suje su killace kansu tukunna sannan za a dibi samfirin su a yi gwajin coronavirus.

Wadanda aka dakatar da ga shiga fadar shugaban kasa sun hada da CPO Lawal Kazaure; Yusuf Sabiu; Musa Daura, Garba Shehu, Babagana Monguno; Ahmad Rufai, Bashir Ahmad da sauran su.

Sai dai a sakon da Garba shehu ya rika sakawa a shafin sa ta tiwita, ya ce dama suna aiki ne ta yanar gizo a ‘yan kwanakinnan.

Wannan jana’iza da Hadiman Buhari suka halarta, ya sa ‘yan Najeriya sun yi tir da cudanyar da suka yi duk da su ne suke kira da a killace kai.

Yan najeriya sun ce lallai dole a killace kuma ayi musu gwajin cutar kafin su yadawa mutane.

Share.

game da Author