CORONAVIRUS: Tsangwamar da ake min don ina bakin fata ba zai sa in karaya ba – Shugaban hukumar WHO

0

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, Tedros Ghebreyesus ya bayyana cewa ana ta kawo masa hari, tsangwama da nuna wariyar launin fata tunda aka fara yaki da annobar cutar coronavirus a fadin duniya.

” Bari in gaya muku, a tsakanin watanni biyu zuwa uku da suka wuce, an rika tsangwama ta da kuma yi min suka da nuna wariya na launin fata saboda kafe wa da nayi sai anyi abinda ya kamata da nuna cewa Nahiyar Afrika ba bola bace.”

” Ina farin ciki da Allah yayi ni bakin fata, tsangwamar da turawa ke min bai dada ni da kasa ba ko kadan. Saboda haka in sun ga dama su ci gaba. mutawa ma ba tsoranta muke ba.”

Tedros ya ce ba zai daina fadin gaskiya ba game da abubuwan da ke faruwa sannan kuma a karkashin shugaban sa, ba zai sa ido ya ga ana ci wa kasashen Afrika fuska kuma yayi shiru don bakaken fata ne ba.

” Kasar Taiwan ne ta fara muzguna min suna tsangwamata da nuna min kiyayya. Hakan bai sa na kauce daga abinda muka sa a gaba ne a wannan aiki na dakile yaduwar cutar coronavirus ba.

Idan ba a manta a makon da ya gabata, Tedros ya soki kiran da wasu likitocin kasar Faransa da suka ce za a fara yin gwajin maganin coronavirus a Nahiyar Afrika ne. Tedros ya ce babu wanda zai yi haka a duniya. Yace kowani jinsi halittan Allah ne kuma kowa ke fama da cutar saboda haka za a bi yadda hukumar WHO ke aiki ne domin yin gwajin maganin idan aka kammala aiki akai.

Share.

game da Author