Akalla kasashe sama da 90 ne suka garzaya Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), au na neman tallafin fita kuncin Coronavirus, bayan da barkewar cutar ta haddasa tattalin arzikin duniya ya kamo hanyar durkushewa gadan-gadan.
Shugabar IMF, kristalina Georgieva ce ta bayyana haka. Ta kara da cewa a tarihin duniya, ba a taba samun yanayin da tattalin arzikin duniya ta tsaya cak kamar a wannan lokacin na Coronavirus ba.
“Matsin tattalin arzikin da mu ke fama da shi a duniya ya kai gargara. Yanzu kasashe kowace neman gwanin ninkaya ta ke yi, wanda zai ceto ta daga nutsewa cikin makeken ruwan da na su iya fitar da kan su.” inji Geogieva.
Daga nan sai ta ce babban abin damuwa da tausayi, shi ne kasashen Afrika da tattalin arzikin su ya dan fara farfadowa, yanzu kuma Coronavirus ta tsinka musu igiyar guga, ta fada rijiya.
Kan haka ne sai IMF ta ce za ta bayar da tallafi na lamunin dala triliyan daya ga kasashe da dama, ciki kuwa har da wasu kasashen Afrika, wadanda idan aka ba su lamunin, to zabi biyu ne rak su ke da shi: Ko dai su ciyar da al’ummar su abincin, ko kuma su bar jama’ar ta su cikin yunwa, su kashe kudaden wajen yaki da Coronavirus.
Daga karshe ya roki kasashe su janye karbar kudaden da suke yi ga al’ummar su kafin a kula da lafiyar su. Ya kuma nemi a rika yi wa jama’a gwaji kyauta.
Najeriya na daga cikin kasashen da tattalin arzikin su ya durkushe, domin ko a ranar Juma’a sai da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya ce Najeriya ta shiga halin da ba ta gaba shiga ba a karkashin gwamnatocin baya.
“Ya kamata mu fito fili mu shaida wa al’ummar kasar nan cewa Najeriya ta rufta cikin mawuyacin halin da ba ta yaba ruftawa ba a karkashin gwamnatocin baya.