Ranar Litinin ne kasar Amurka ta girgiza da labarin rasuwar likitan likitocin kasar, wanda ya fi kowa kwarewa wajen aiktin tiyatar raba jariran da aka haife su amma kawunan su manne da juna.
James Goodrich ya mutu ne bayan ya kamu da cutar Coronavirus, kamar yadda gidan talbijin na CNN ta bayyana a ranar Litinin.
Sunan Goodrich ya fito a duniya a cikin shekarar 2004, inda ya kyale CNN ta dauki wata tiyata da ya yi kai tsaye aka nuna a duniya. Wato tiyatar wasu yara tagwaye biyu, ‘yan kasar Philippines, Jadon da Annias MCDonald.
Goodrich ya dabbaka hikima da basirar raba yaran da aka haifa kan su har ma da kwakwalwar su na manne da juna. Wannan ya janyo masa suna da zuhuri a duniya. Sannan kuma ya kara samun karin jini kasancewa mutum ne mai tausayin kananan yara.
Goodrich kan maida yaran da ya yi wa tiyata matsayin abokan sa. Ya kan ziyarce su har gida ba tare da sun san zai je ba. Sannan kuma ya na yi wa yaran da ya yi wa tiyata ziyarar-bazata a ranar bikin tunawa da ranar haihuwar su.
CNN ta bayyana yadda hankalin Shugaban Babban Asibitin Montefiore, ya tashi matuka bayan rasuwar Goodrich. Shugaban mai suna Philip Ozuah ya ce an yi babban rashin da ba ya misaltuwa.
Cikin shekarar 2004 ne Goodrich ya yi nasarar yi wa tagwayen tiyata ya raba kwakwalwar su da kuma kan su.
Cikin shekarar 2016, Goodrich ya jagoranci gungun wasu kwararrun likitoci 40, inda suka shafe sa’o’i 27 suka yi nasarar yin tiyatar raba wasu yara ‘yan shekara daya, wadanda aka haife su kan su da kwakwalwar su na manne da juna.
Wannan ne karo na bakwai da Goodrich ya yi irin wannan tiyata, kuma ita ce ta 59 tun daga shekarar 1952 da aka fara samun nasarar irin wannan tiyata.
Goodrich ya yi aiki wurare da dama, ciki har da kasancewar sa babban likita a Kwalejin Ilmin Kirkirar Magunguna ta Albert Einstein.
Cutar Coronavirus ta kashe likitoci da dama a duniya. A kasar Chana inda cutar ta fara bulla, likitoci sama da 3,000 ne suka kamu da cutar, yayin da ta kashe likitoci 60 a Italy.
Discussion about this post