Hukumar Kula da Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana cewa cutar COVID-19, wato Coronavirus, ta fallasa rashin ingancin tsarin kula da lafiya na kasashen duniya da dama.
Babban Daraktan WHO, Tedros Ghebreyesus ne ya bayyana haka a wani taron ganawa da manema labarai karshen makon nan.
“Wannan cuta wadda kafin watanni uku baya ba a san ta ba, ta nuna cewa kasashe da dama ba su da kyakkyawan tsarin kula da lafiya. Sannan kuma bayan ta bulla, kasashen da ake ganin su ne wasu fitattu a harkar kiwon lafiya, sun kasa yin wani gagarimin shirin hana cutar yin tasiri.” Cewar sa.
“Ya kamata a rika tashi tsaye ana aiwatar da shirye-shirye masu kaiwa ga mafita. Domin iya annoba, musamman wadda ke kisa, idan ta ritsa mutane, to kisan rundugu ta ke musu.
Shugaban na WHO ya ce an koyi darasi sosai daga bayan an da kasaahen China, Koriya ta Arewa suka bayyana dangane da yadda suka sha gaganiyar shawo kan cutar.
Da ya ke magana a kan kudaden neman agaji da WHO ta kafa gidauniyar neman taimako na dala milyan 677, ya ce an tara kudaden, an kuma raba su a inda ya dace domin yaki da cutar Coronavirus a fadin duniya.
Idan ba a manta ba, lokacin kaddamar da Gidauniyar, Tedros ya ce ya damu da kasahen Afrika sa sauran wadanda ba su da ingantaccen tsarin kula da lafiya.
Sai dai kuma ya ce akwai bukatar karin kudaden saboda tun daga watan Fabrairu masu kamuwa da cutar sai kara yawa su ke yi.
Tun ranar Jama’a adadin wadanda cutar ta kama a duniya ya kai sama da milyan daya, sannan kuma ta kashe sama da mutum 50,000.
Discussion about this post