CORONAVIRUS: Shugaban Ghana ya ce kowa ya sha ruwa na wata uku kyauta, kuma ya haramta dauke wuta

0

Shugaban Ghana Nana Akufor-Addo, ya umarci Hukumar Bayar da Ruwa ta Kasar Ghana cewa ta bar kowane dan kasar ya sha ruwa kyauta, har tsawon watanni uku.

Ya yi wannan bayani a ranar Lahadi a cikin jaqabin da ya ke yi wa al’ummar kasar akai-akai, dangane da halin da Ghana ke ciki wajen kokarin dakile fantsamar Coronavirus a kasar.

Wannan ne jawabin sa ba biyar, run bayan da aka samu bullar cutar Coronavirus a Ghana.

Addo ya kuma gargadi hukumar kula da lantarki ta kasar cewa kasa ta sake ta yanke wa kowa wutar lantarki, kuma kada kada ta dauke wa mutanen gari bai-daya.

Ya ce gwamnati ta dauke wa jama’a kowa da kowa kudin ruwa na watannin Adrilu, Mayu da Yuni. Kuma ya ce Hukumar Ruwa ta hada kai da masu tankokin ruwa na gwamnati da masu zaman kan su, domin a tabbatar cewa an wadatar da ruwa har a cikin yankunan da ke fama da matsalar ruwa ko kuma yankunan marasa kardu.

Da ya koma kan yaki da cutar Coronavirus a Ghana, shugaban ya ce ya zuwa yau an zakulo mutum 19,276, wadanda gwamnati ta tabbatar cewa sun cakudu da wadanda suka kamu da cutar Coronavirus.

Ya ce ana kan yi wa mutum 15,384 gwaji. Wannan sakamakon gwaji ne zai iya nuna cewa ko za a janye dokar hana walwala ko ba za a janye dokar ba.

Ghana na cikin kasashen Afrika wadanda cutar ta fantsama a cikin su. Mutum 214 suka kamu, yayin da aka tabbatar da mutuwar mutum biyar.

Share.

game da Author