CORONAVIRUS: Sanata Ndume ya ce akwai damfara da rub-da-ciki a Kwamitin Rabon Agaji, ya nemi a rusa Kwamitin

0

Sanata Ali Ndume daga Jihar Barno, ya zargi Kwamitin Rabon Kayan Tallafin Rage Radadi Lokacin Coronavirus, wanda ke karkashin Ministar Harkokin Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma, Sadiya Umar, da tabka almundahana, harkalla da rub-da-ciki.

A kan haka ya ce yadda suka yi rabon kayan agajin ya nuna cewa bai kamata a damka wa kwamitin aikin rabon makudan kudade irin wannan, don haka ya yi kira da a rusa kwamitin kawai.

Ndume, wanda ke wakiltar Mazabar Sanatan Barno ta Kudu, ya ce idan dai ba Shugaba Muhammadu Buhari ya na so a kifar masa da dan sauran kima da mutuncin sa da suka rage a cikin yashi ba, to ya gaggauta kwace rabon kudi da kayan agaji daga hannun kwamitin da Sadiya Farouq ke shugabanta.

Ndume ya ce ya ji haushin Shugaba Buhari jin yadda ya kammala jawabin sa baya-bayan nan, amma bai ambaci rusa kwamitin rabon kudin tallafin ba.

Da ya ke hira da manema labarai a Maiduguri, Ndume ya ce idan dai wannan shiriritar da badakala na harkallar da ake yi, ita ce rabon kudin tallafi, to gara ma kada a ci gaba kawai, saboda sun maida harkar rabon tallafin harkalla kawai.

Ya ce kuma shi ba zargin Minista din ko wasu ‘yan kwamitin ya ke yi ba. Duk maganar da ya ke yi, ya na da tulin hujjoji.

“Mu na ci gaba da samun korafe-korafe a kan yadda kwamitin rabon tallafi ke harkalla. A rage wa Shugaba Buhari ya rusa kwamitin tun kafin su rusa masa sauran mutuncin sa.”

Daga nan sai ya yi kira da a kafa sabon kwamitin wanda za a fito da wakilai daga sassa daban-daban na kasar nan da kuma wakilai da ga hukumopmon tsaro da Majalisar Tarayya da kuma jami’an Harkokin agaji daga kowace jiha. Kuma a samu wakilai daga kungiyoyin sa-kai masu rajin kare hakkin jama’a.

“In banda harkalla, ya za a ce Jihar Zamfara inda Minista Sadiya ta fito, za a ce an yi wa fakirai 1, 341,153 rajista a gidaje 291,629, ya zuwa 20 Ga Maris.

“Amma Sokoto gidaje 3,347 kadai, kuma mutum 18,435 kacal. Barno gidaje 7,130, Kula mutum 33,728 kacal.

“Mu na kwararan hujjoji da suka tabbatar da cewa sun rika tattaro sunayen bogi. Mutum daya sai ta rubuto sunayen dubban mutane, ya hada baki da dibgaggun jami’an banki a kirkirar musu lambar BVN. Kuma idan aka yi bincike za a tabbatar da haka.

“Sun maka sunayen masu dafa musu abinci, na direbobin su, na dangin su, na dangin boyi-boyin su da ka sauran masu yi musu hidima. Wai su ne tantiran fakiran da su ka cancanci a raba wa tallafin.” Inji Ndume.

A hirar da aka yi da ita a gidan talbijin na TVC, Sadiya Farouq ta kare kan ta da kwamitin ta, inda ta ce duk abin da su ke yi, a bisa ka’ida su ke yi, babu harkalla a ciki.

Kokarin jin ta bakin Hadimin ta a Fannin Yada Labarai, Salisu Dambatta ya ci tura, domin cewa ya yi a tura masa tambayoyi ta WhatsApp.

Share.

game da Author