Hukumar NCDC ta mika wa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje sakamakon gwajin jinin sa da aka yi na coronavirus.
sakataren yada Labaran gwamna Ganduje Abba Anwar ya bayyana a takarda da ya fitar ranar Alhamis cewa gwajin ya nuna cewa Ganduje bashi da cutar coronavirus.
Ba shi Kadai ba har da matar sa da ita ma aka yi gwajin jinin ta bata da da cutar.
” Muna yi wa Allah godiya da ya kubutar da gwamnan mu da matar sa daga wannan cuta. Muna gode wa Allah da kuma yin yabo a garesa. kuma muna rokon Allah ya baiwa wadanda suka kamu da cutar Lafiya ako ina suke a fadin duniya, ya kuma ci gaba da kare mu.
Bayan haka gwamna ganduje yayi kira ga mutanen jihar cewa a rika kiyaye dokoki da shawarwarin da ma’aikatar kiwon lafiya ta bada game da kare kai daga wanna cuta.
A rika yawan wanke hannu da sabulu sosai, sannan a nesanta kai daga shiga cunkoson jama’a. Sannan a rika zama a gida idan ba ya zama dole a fita bane ‘ Hakan shine ya fi dacewa ayi.”
Daga karshe ya gargadi masu karya doka cewa gwamnati zata hukunta duk wanda yaki bin doka da oda. sannan ya yaba wa ma’aikatan kiwon lafiya kan ayyukan da suke yi a fadin jihar tun bayan bayyanar cutar a jihar.