Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta yi wasu daurarru 2600, domin kauce wa cunkoson kamuwa da cutar Coronavirus a kasar nan.
Da ya ke jawabi a Hedikwarar Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku ta Kasa, Aregbesola ya ce wanan afuwa da aka yi musu ta na bisa tsarin rage yawan cinkoso a gidajen kurkuku ne da aka ce za a yi, ganin yadda cutar Coronavirus ta bulla gadan-gadan a Najeriya.
Ga wadanda za a yi wa Afuwa
Jaridar Punch ta ruwaito Aregbesola na cewa rukunin daurarrun da za a yi wa afuwa, sun hada:
1. Daurarrun da suka shekara 60 a duniya abin da ya yi sama.
2. Daurarru marasa lafiya, kuma a bisa dukkan alamu rashin lafiyar ta su a iya cewa ciwon ajali ne.
3. Wadanda aka yanke wa hukuncin daurin shekara uku abin da ya yi sama, sannan kuma bai fi watanni shida su kammala wa’adin daurin na su a kurkuku ba.
4. Daurarrun da ciwon tabin hankali ya same su.
5. Daurarrun da aka yanke wa zabin biyan diyyar da ba ta wuce naira 50,000 ba, amma suka kasa biya.
Wadanda ba za a yi wa Afuwa ba
Minista ya ce su ne rukunin daurarrun da aka kama da manyan laifuka irin su ta’adda ci, fashi da makami, gsrkuwa da mutane, kisa da kuma fyade.
Ya kara da cewa za a saki fursunonin farko daga kurkukun Kuje da ke Abuja. Daga nan kuma za a tsara yadda yadda za a ci gaba da sakin sauran a kurkukun fadin kasar nan.
Shi ma Ministan Shari’a Malami, ya ce zai ci gaba da yin afuwar kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta shawarci kowace kasa ta rage yawan daurarru domin a rage cunkoso a gidajen kurkuku, ganin yadda annobar Coronavirus ta barke a duniya.
Discussion about this post