CORONAVIRUS: PDP ta nemi a daina cire wa mutane harajin ATM

0

Jam’iyyar PDP ta nemi Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin bankuna su daina cire wa jama’a kudi idan sun yi amfanin da katin su na ATM sun ciri kudi ko sun aika da kudi zuwa wani asusun banki.

Haka nan kuma PDP ta ce saboda a rage wa jama’a radadin kuncin zaman gida, a wannan lokacin, saboda gudun kamuwa da Coronavirus, ya kamata a dakatar da cire wa kwastomomi kudade idan sun yi amfani da wayoyin su ko suka tura kudade, ko su ka biya kudin wuta da dai sauran wasu mu’amaloli da ake yi ana tasarifi ko hada-jadar kudade da wayar hannu.

Kakakin Yada Labarai na Jam’iyyar PDP, Kola Olagbondiyan ne ya bayyana haka a cikin wata takardar da ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce dakatar da cirar wadannan guntattakin kudade zai iya zama wata karin hangar saukake wa jama’a halin kunci da zaman takura da su ke ciki.

Daga nan ya yi kira ga CBN ya gaggauta umartar dukkan bankunan kasar nan, su daina cirar kudaden da sunan haraji, har zuwa lokacin da aka wuce wannan mawuyacin hali na annobar Coronavirus.

A dakatar da biyan kudin lantarki

Olagbondiyan ya ce ya kamata a dakatar da biuan kudin wuta, musamman a yankuna da unguwannin da talakawa ne su ka yi kaka-gida.

Idan aka dakatar da yanke wa talaka wuta, kuma aka dakatar da karbar kudin wuta a hannun sa, to zai ji sauki a wannan yanayi da aka ciki.

A karshe ya nemi gwamnati ta tattara bayanan sunayen masu kananan sana’o’i daban-daban, domin su ma a taimaka mu su.

Share.

game da Author