Dan wasan Arsenal Mezut Ozil, kuma dan kasar Jamus, ya hada kai da wasu ‘yan wasan Chelsea inda suka fara tara kudade domin sayen kayan kariya daga cutar Coronavirus su aika da su kasar Saliyo da ke nan Afrika.
Sun yi wannan hadakar gidauniya ce bayan samun labarin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar cewa akwai kasashe a Afrika wadanda ke bukatar tallafi, kuma idan ba a hanzarta ba, to cutar za ta yi musu mummunan kisa kila ma fiye da yadda ta yi a kasashen Turai.
Ozil ya hada kai da Antonio Rudiger, wanda haifaffen Jamus ne, amma iyayen sa Mathias da Lily ‘yan kasar Saliyo ne.
Sun hadu da juna a Jamus bayan kowanen su ya arce daga Saliyo cikin 1991, sakamakon yakin basasa.
Kafafen sadarwa sun ruwairo su Ozil na cewa za su aika da tulin kayan da za su saya a hannun iyayen dan wasan na Chelsea, Rudiger, wato Mathias da Lily.
Wani abin birgewa kuma shi ne yadda Kungiyar Tarayyar Turai ta shiga cikin lamarin, ta alkawarta cewa duk abin da Ozil ya bayar gudummawa, ita ma za ta bayar da haka.
Haka nan za ta bayar da gudummawar duk abin da Kante, Rudiger ko Geroud suka bayar a matsayin gudummawar ta a gidauniyar.
Ozil na ci gaba gada da samun yabo da jinjina a Ingila, tun bayan wannan hakan kan ‘yan wasa da ya yi domin a agaji Saliyo.
Idan ba a manta ba, kwanan nan wasu tsoffin ‘yan kwallo a Ingila sun goyi bayan Ozil, bayan da ya ji yarda kungiyar Arsenal ta zabtare masa albashi saboda kuncin Coronavirus.
Ozil ya na karbar albashin €350,000 a kowane sati.
Idan aka maida albashin Ozil zuwa naira, a kowane sati ya na daukar naira milyan 168 kenan.