Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar dawo da ‘yan Najeriya da ke makale a kasshen waje, wadanda suka kasa dawowa gida saboda dakatar da zirga-zirgar jiragen.
Yayin da kasashe da dama suka hana shiga da mutane ko dabbobi da tsuntsaye daga wata kasa zuwa wata, ita kuwa Najeriya ta shirya jajibo wasu ‘yan kasar ta daga wasu kasashe, a daidai lokacin da cutar Coronavirus ta ragargaza kasashen da suke a makale, kuma cutar a yanzu ta karkato zuwa Najeriya.
Yayin da aka shirya dawo da su, Gwamnatin Shugaba Buhari ta ce kowa shi zai biya kudin tikitin jirgin da za a maido shi Najeriya.
A kan haka ne Najeriya ta umarci ofisoshin jakadun ta da ke kasashe daban-daban su fara tattara sunayen wadanda ke da bukatar dawowa gida.
Shugabar Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana cewa gwamnari ba za ta dawo da kowa da kudin aljibun ta ba. Don haka kowa ya tanaji kudin tikiti.
Haka dai wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na hukumar, Abdul-Rahman Balogun ya bayyana
a cikin wata takarda da ya sa wa hannu a madadin Shugabar Hukumar.
Dabire ta ce kulle kasashen da ‘yan Najeriya ke makale a can ne ya sa wadanda ke ganin a takure su ke a can ke ta kewar dawowa gida.
Ma’aikatar Harkokin Kudade ta Najeriya ce ta sanar wa Dabire cewa ta shaida wa masu son dawowar ba za kwaso su ko dawo da su kyauta ba.
Sai An Killace Su Kafin Kowa Ya kama gaban sa. Daga nan sai ta umarci duk mai sin dawowa, to ya je ya bada bayanan sunayen sa a ofishin jakadan Najeriya da ke kasar da ya ke a makale.
Sai dai kuma duk da kudin su za su kashe a kawo gida ba kyauta za dawo da su ba, Dabire ta ce su gode wa Gwamnatin Buhari da wannan karimci da ya ta yi musu.
Sanann ta bayar da lambar adireshin rumbun tattara bayanan da za su shiga ta intanet su cika fam a saukake, saboda yawancin kssashen da suke a makale duk an Killace kowa a gida, babu zirga-zirga.
Sai dai kuma a nan Najeriya mutane da dama na kokawa da wannan abin da suke ganin cewa ganganci ne karara, domin bai kamata a dauko abin da suka kira kara-da-kiyashi a shigo da shi a wanann hali ko yanayi da duniya ke ciki ba.