CORONAVIRUS: Najeriya ta kaddamar da Tsarin Koyon Darussa Da Fasaha ta yanar gizo daga Gida

0

Sakamakon yadda dokar zaman gida ta gurgunta shirin karatu a kasar nan, Najeriya ta kaddamar da Tsarin Daukar Darussa da Koyon Fasaha ta Intanet daga gida.

Kamar yadda Ministan Sadarwa Isa Pantami ya bayyana, ya ce an kirkiro shirin ne domin matasa musamman dalibai da wadanda ma ba dalibai ba, su samu damar yin nazarin wasu tsare-tsaren kwasa-kwasai daga gida ta Intanet, yadda za su kara inganta fasahar su da dabarun sadarwar zamani.

Gwamnatin Tarayya ta rufe makarantun kasar nan tun farkon barkewar cutar Coronavirus.

Sai dai kuma ganin yadda aka fara dadewa ba a fito da wani tsarin manhajar da dalibai za su ci moriyar zaman gidan da su ke yi ba, ta hanyar ba su ilmi, sai iyayen yara suka rika sukar dadewar da yaran suka yi su na zaman-dirshan a gida.

Amma a ranar Labara sai Minista Pantami ya kaddamar da tsarin Koyon wasu darussa daga gida ta Intanet a wata ganawar su da Hukumar Inganta Fasahar Sadarwar Zamani (NITDA).

Pantami ya ce fito da shirin wa wannan lokaci ya zama wajibi domin aka inganta wa matasa hanyar kara gogewa da kwarewa ta hanyar Koyon wasu darusa ta intanet daga gida.

Za a fito da tsarin kwasa-kwarai na karin gogewa da kwarewa ta hanyar watsa manhaja da rumbunan tara bayanan da matasa za su rika shiga su na koyo a intanet.

Pantami ya ce kwmfanoni irin su CISCO, Oracle da Huawei kai har ma da Harvard duk za su bayar da aatifiket na shaidar shiga shirin ga matasa.

Pantami ya kara da cewa su na kokarin kafa wa Majalisar Zartaswa ta Kasa (FEC) wannan tsari na gudanar da ayyuka daga gida a saukake, yadda Shugaban Kasa ko daga gida zai iya gudanar da taro tare da Ministocin sa, ba tare da sun yi haduwar gangami wuri daya ba.

Shugaban NITDA, Kashifu Abdullahi ya ce an kaddamar da wannan tsari saboda kuncin da cutar Coronavirus ta haifar a cikin al’umma.

Shi kuma wakilin kamfanin Oracle a Najeriya, Olakunle Olatimeyi, ya yi kiran gwamnati ta jawo kamfanonin layukan wayoyi a cikin lamarin, ta yadda za su rika wa matasa da dalibai data cikin sauki, domin su rika samun rahusar shiga intanet su na nazari a manhajojin tsarin koyon darussan.

Share.

game da Author