Coronavirus na ci gaba da fantsama a Najeriya, mutum 223 sun kamu cikin mako daya

0

Yayin da aka fita cikin mako jiya, alkaluman kiddiddigar masu dauke da cutar Coronavirus sai ci gaba da yawa su ke kara yi, maimakon su rika raguwa.

Dukkan kayan aikin da Hukumar Kula da Cututtuka ta kasa ta samu, an kasa, wannan bai sa masu kamuwa da cutar na raguwa ba.

Cikin mako da ya gabata an samun karin mutum 223. Wannan kuwa abin tayar da hankali ne matuka.

Adadin wadanda suka kamu 223 da aka samu a cikin mako daya, shi ne adadi mafi yawa cikin mako daya.

Kafin sannan kuwa, mafi yawan adadin mako daya shi ne mutane 104 da suka kamu a tsakanin 5 zuwa Ga Afrilu.

Daga cikin mutum 542 da suka kamu ya zuwa ranar Asabar, kashi 41% bisa 100% duk a ciki n makon da ya gabata suka kamu.

Lagos ke da mutum 306, Abuja 81, Kano 37, Ogun 19, Oyo 16. Abin mamaki shi ne yadda jihohin Kudu Maso Gabas, har yau cutar ba ta isa gare su sosai ba. Jihar Enugu ce mai mutum biyu suka kamu da cutar.

Shugaban NCDC ya ce shi ya na ganin karin yawan masu cutar da ake ci gaba da samu, ya na da nasana da yasan gwaje-gwajen da ake kan yi sosai a yanzu.

A Najeriya dai jihohi 19 da kuma Abuja ne cutar ta fantsama.

Wannan babban abin damuwa ne, idan aka yi la’akari da cewa, kwanaki biyu baya, Shuhaban NCDC, ya ce Coronavirus za ta mamaye Najeriya baki daya -Shugaban Hukumar Kula da Cututtuka

Shugaban Hukumar Kula da Dakile Cututtuka ta Kasa (NCDC), Chikwe Ihekweazu, ya jaddada cewa babu wani tsimi, kuma babu wata dabara, sai cutar Coronavirus ta mamaye jihohin Najeriya 36 da Abuja.

Da ya ke magana a gidan talbijin na Channels, safiyar Alhamis, a wani shirin “Sunrise”, Chikwe ya ce, ” Coronavirus za ta fantsama zuwa kowace jiha a kasar nan. Ai kamar cutar Zazzabin Lassa ce.

“Sai dai ita Zazzabin Lassa ba a kulle garuruwa ba, saboda ba ta da karfi kamar Coronavirus.

“Dalili kenan duk da ba a killace mutane a gida ba, mu ka yi nasarar shawo kan ta. To yanzu ana maganar Coronavirus. Cutar nan mu shirya sai ta mamaye jihohin kasar nan kalaf. Saboda babu wani dalili ko tawilin da wani zai iya kawowa, ya ce cutar ba za ta fantsama ko’ina ba.”

Da ya koma kan nasarar da ake samu a yanzu, ya ce an kafa na’urorin bincike a Kano, kuma wannan ya bada damar ana samun yin bincike sosai ka cikin lokaci.

Sai dai kuma ya yi tsokaci dangane da yadda aka samu masu dauke da cutar har mutum 34 a ranar Laraba, adadin da ya ce shi ne mafi yawa da aka samu a rana daya, fum lokacin da cutar ta bazu a Najeriya.

Sama da mutum milyan biyu suka kamu da cutar a duniya. Yayin da ta kashe sama da mutum 100,000. Jihohi da dama na Najeriya na ci gaba da hana zirga-zirga, kamar yadda dokar za ta fara aiki a ranar Alhamis da dare a Kano.

A karon farko dai an samu rahoton cutar ta kashe mutum daya a Kano, bayan sama da mutum goma ne aka bada rahoton sun kamu, a birnin mafi girma a kasar, in banda Lagos.

Shugaban na Hukumar NCDC, ya ce babbar nasarar da su ke samu ita ce, “duk da fantsamar da cutar ke kara yi, su na zakulo masu dauke da ita, su na gwaji, su na killace masu cutar, kuma ana ci gaba da samun masu warkewa sosai.”

Share.

game da Author