Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya sanar cewa mutum uku dake dauke da cutar Coronavirus sun mutu a jihar.
Mai ba gwamna Tambuwal Shawara kan harkokin yada labarai, Muhammed Bello ya bayyana haka a takarda da ya rabawa manema Labarai.
Tambuwal ya kara da cewa wadanda suka mutu duk suna da manyan cututtuka a jikin su baya ga Coronavirus, kamar hawan jini, Asma, ciwon siga da sauransu.
Kwamishina kiwon lafiyar jihar Sokoto Mohammed Inname ya ce jihar ta samu karin mutum takwas da suka kamu da cutar. Yanzu mutum 10 kenan suka kamu da cutar a jihar Sokoto.
Saidai kuma ya ce ana nan ana yin bincike kan yadda cutar ta fado jihar, domin kamar yadda Inname ya fadi wanda aka fara samu dauke da cutar bai yi tafiya ko ina ba.
Ya ce gwamnati da ma;aikatar sa za su ci gaba da bin diddigin haka da kuma yin farauta, killace da yin gwajin wadanda ake zaton sun yi cudanya da wadanda ke dauke da cutar a jihar.