Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Talata.
A bayanan da NCDC ta fitar ranar Talata, Legas ta samu karin mutum 74, Abuja 1, Katsina 5, Ogun 4, Delta 2, Edo 2, Kwara 1, Oyo 1, Adamawa 1.
Yanzu mutum 873 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 197 sun warke, 28 sun mutu.
Lagos-430
FCT-118
Kano-73
Osun-20
Ogun-20
Oyo-16
Katsina-16
Edo-15
Kwara-9
Kaduna-9
Akwa Ibom-9
Borno-9
Bauchi-8
Gombe-5
Delta-4
Ekiti-4
Ondo-3
Rivers-3
Jigawa-2
Enugu-2
Niger-2
Abia-2
Benue-1
Anambra-1
Sokoto-1
A sakamakon gwajin da ya fito ranar Talata, Jihar Legas ce kan gaba wajen yawn wadanda suka kamu da cutar, Sai kuma babban birnin Najeriya, Abuja.
Jihar Kano ma ta ci gaba da kawo maki mai yawa da har yanzu itace jiha ta uku da tafi yawan wadanda suka kamu.
Jihar Barno ma ta samu mutum dcaya cikin wadanda a ka fidda sakamakon gwajin su ranar Talata.