Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Juma’a.
A bayanan da ta fitar, Jihar Kano ta samu karin mutum 6, Legas 32, Abuja 2, 5 a Kwara, Oyo 2, Katsina 2, 1 a Ogun da 1a Ekiti.
Yanzu mutum 493 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 159 sun warke, 17 sun mutu.
Lagos- 283
FCT- 69
Kano- 27
Osun- 20
Edo- 15
Oyo- 15
Ogun- 10
Katsina- 9
Bauchi- 6
Kaduna- 6
Akwa Ibom- 6
Kwara- 9
Delta- 4
Ondo- 3
Enugu- 2
Ekiti- 3
Rivers-2
Niger- 2
Benue- 1
Anambra- 1
Idan ba a manta ba shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) Chikwe Ihekweazu ya koka kan yadda mutane ke kyamatar wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.
Ihekweazu ya fadi haka ne a zaman da kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar COVID-19 ya yi a Abuja ranar Alhamis.
Ya ce nuna wariya da ake yi wa wadannan ke dauke da cutar na dawo wa hukumar da hannun agogo baya a aiyukkan da suke yi na hana yaduwar a Najeriya.
Ihekweazu ya ce NCDC na kokarin ganin ta kara yawan mutanen da ake yi wa gwajin cutar a kasar nan amma hakan ba zai yiwu ba idan ana ana kyamatar su a duk inda suke.
Ya ce mutane za su fara guje wa yin gwajin cutar da boye wa ma’aikatan kiwon lafiya saboda haka.
Discussion about this post