Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Alhamis.
A bayanan da ta fitar, Jihar Kano ta samu karin mutum biyar, Legas 19, Abuja 9, Oyo biyu.
Yanzu mutum 442 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 152 sun warke, 13 sun mutu.
Lagos- 251
FCT- 67
Kano- 21
Osun- 20
Edo- 15
Oyo- 13
Ogun- 9
Katsina- 7
Bauchi- 6
Kaduna- 6
Akwa Ibom- 6
Kwara- 4
Delta- 4
Ondo- 3
Enugu- 2
Ekiti- 2
Rivers-2
Niger- 2
Benue- 1
Anambra- 1
Ministan Harkokin Lafiya, Osagie Ehanire, ya shawarci jama’a su juri yin amfani da takunkumin rufe baki da hanci ko hankici ko wani dan kyalle su na rufe bakin su da hanci, domin rage yiwuwar kamuwa da cutar Coronavirus.
Ehanire ya yi wannan karin hasken ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi a ranar Litinin a Abuja.
Ya ce wadannan hanyoyi ne na rage yiwuwar kamuwa da cutar, musamman idan mutum ya shiga cikin Jama’a.
“Rufe hanci da baki da takumkumi ko hankici ko wani kyalle kan hana feshin miyau shiga hancin mutum, ko wani burtsatsin kwayoyin cuta daga bakin mai magana da karfi a kusa da mutum. Kai ko wani idan ya yi gwaron numfashi kusa da kai. Ko wanda ya balgace da dariya da karfi. Ko wanda ya hangame baki ya na magana da karfi.
“Daura wannan takunkumi na da amfani a inda shiga jama’a ya zama tilas, musamman a cikin kasuwa.
“Sai dai kuma saboda irin takunkumin da mu ke amfani da shi, wanda ake amfani da shi ne a rana tal. Ana jefar da shi a kwandon shara na da ya kwana daya.
Discussion about this post