Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da Karin mutane 19 da suka kamu da Coronavirus a Najeriya ranar Talata.
An gano mutane 19 ne a jihohin 4 da Abuja.
Mutum 14 a Legas, 1 a Kano, 1 a Edo, Akwa Ibom 1 sannan 2 a Abuja.
362 – Suka kamu zuwa yanzu
99 – Aka Sallama
11 – Sun mutu
Jihar Legas na da mafi yawan mutanen da suka kamu da cutar a Najeriya.
Lagos- 203
FCT- 58
Osun- 20
Edo- 15
Oyo- 11
Ogun- 9
Bauchi- 6
Kaduna- 6
Akwa Ibom- 6
Katsina-5
Kwara- 4
Ondo- 3
Delta- 3
Kano -4
Enugu- 2
Ekiti- 2
Rivers-2
Benue- 1
Niger- 1
Anambra- 1
A dalilin karuwa da ake samu na yawan mutane da suka kamu da cutar coronavirus a Kano. Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya Sanar da saka dokar zaman Gida dole na kwana bakwai a fadin jihar.
Gwamnati ta saka wannan doka a dalilin sake bankado wani a jihar da ya kamu da Cutar.
Discussion about this post