Hukumar Hana Haduwar cututtuka ta kasa NCDC, ta bayyana cewa mutum 17 sun kamu da cutar coronavirus a sakamakon gwajin ranar Juma’a.
An samu karin mutum 17 daga jihohi 6 da Abuja a Najeriya.
8 a jihar Legas, 2 a Abuja, 1 a Kaduna, 3 a Katsina, 1 a Niger, 1 a Ondo sannan da 1 a Anambra.
Hukumar ta ce mutum 58 sun warke, 7 sun rasu.
Legas -163
FCT – 56
Osun – 20
Oyo – 11
Akwa Ibom – 5
Ogun – 7
Edo – 12
Kaduna – 6
Bauchi – 8
Enugu – 2
Ekiti- 2
Ribas – 2
Benuwai – 1
Ondo – 2
Kwara – 2
Delta – 2
Katsina – 4
Niger – 1
Anambra – 1
Akalla gwamnonin Najeriya shida ne suka wancakalar da dokar hana taro a jihohin su suka ba mutane daman a cakude kawai duk da dokar hana haka da gwamnatin tarayya saka kuma tayi kira a kan abi.
Gwamnonin Najeriya sun ba mutane dama su ci gaba da halartar wuraren bautar su da ya hada da coci-coci da masallatai domin yin ibada ba tare da la’akari da coronavirus da gwamnati ke kokawa da ba a kasar nan da fadin duniya.
Babban hanyar da ake iya dakile yaduwar cutar coronavirus shine kaurace wa gungun jama’a. Idan aka yi haka za a rage yada cutar.
Discussion about this post