CORONAVIRUS: Mutum 114 sun kamu a Najeriya, Yanzu 1095

0

Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Alhamis.

A bayanan da NCDC ta fitar ranar Alhamis, Legas ta samu karin mutum 80, Abuja 5, Zamfara 2, Ogun 1, Gombe 21, Kaduna 1, Edo 2, Oyo 1, Ogun 1, Sokoto 1.

Yanzu mutum 1095 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 208 sun warke, 32 sun mutu.

Lagos-657
FCT-138
Kano-73
Ogun-35
Gombe-30
Katsina-21
Osun-20
Edo-19
Oyo-18
Borno-12
Kwara-11
Akwa Ibom-11
Kaduna-10
Bauchi-8
Delta-6
Ekiti-4
Ondo-3
Rivers-3
Jigawa-2
Enugu-2
Niger-2
Abia-2
Zamfara-2
Sokoto-2
Benue-1
Anambra-1
Adamawa-1
Plateau-1

Jihar Zamfara ta shiga sawun jihohin dake fama da cutar coronavirus. Jihar Gombe ta samu mutum 12 a gwajin ranar Juma’a.

Bayan haka ministan kiwon lafiya, Ehinare Osagie ya bayyana cewa ana samun yawan yaduwar cutar yanzu a unguwanni ne da uraren da jama’a suke.

Ya ce wadanda suka kamu da cutar sun rika cakuda da wadanda basu kamu da cutar ba. Wannan shine babban matsala da ake samu a yanzu

Share.

game da Author